Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 14 ga Watan Maris, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 14 ga Watan Maris, 2019
1. Ekweremadu ya zargi Shugaba Buhari da jinkirtan gabatar da kasafin kudi
Mataimakin shugaban Gidan Majalisa tarayya, Ike Ekweremadu ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da jinkirta wajen gabatar da kasafin kudi a cikin shekaru hudu da yayi mulki.
Ekweremadu ya fadi hakan ne akan zaman tattaunawa da gidan majalisar ta yi akan kasafin kudin shekarar 2019 na kimanin naira Tiriliyan (N8.83) a gabatarwan jagoran majalisar, Sanata Ahmed Lawan, a ranar Talata da ta gabata.
2. Hukumar JAMB ta gabatar da ranar da za a fara jarabawan JAMB ta bana
A jiya Laraba, 13 ga watan Maris 2019, Hukumar JAMB ta gabatar da ranar da za a fara jarabawan shiga makarantan jami’a (JAMB) ta shekarar 2019.
Hukumar JAMB ta gabatar ne da hakan a wata sanarwa da aka bayar ranar Laraba daga hannun mai sanarwa ga hukumar, Mista Fabian Benjamin, da cewa za su fara jarabawar JAMB ranar 11 ga Watan Afrilu, shekara ta 2019.
3. Hidimar banza ce zaben Tarayya ta shekarar 2019 – inji Femi Falana
Lauyan Yaki da Daman Al’umma, Mista Femi Falana (SAN) ya gabatar da haushin sa ga zaben tarayya ta kasa da aka gudanar a makonnan da suka gabata a kasar Najeriya.
A wata zaman tattaunawa da Lauyan, Mista Femi yayi da wata gidan Talabijin, ya bayyana da cewa zaben bana hidima ce ta shiririta da haushi.
4. Gabatarwan Sanata Melaye akan zaben 2019 ya tayar da hargitsi a gidan majalisa
Wata bayanin kallubalai da Sanatan da ke wakilcin yankin Jihar Kogi, Sanata Dino Melaye ya tayar a gidan Majalisar Dattijai ya tayar da hargitsi tsakanin ‘yan gidan majalisar a zaman su ta ranar Laraba da ya gabata.
Hargitsin ya tashi ne a yayin da Sanatan ya kafa baki ga zancen zaben tarayya da aka yi a kasar daga ranar 23 ga watan Fabrairu 2019. Sanatan ya bayyana da cewa anyi amfani da jami’an tsaro don makirci ga zaben.
5. An rasa rayuka da dama a harin da ‘yan ta’adda suka kai wa Ofishin ‘Yan Sanda a Jihar Edo
Rahoto ya bayar da cewa mutane da dama suka rasa rayukar su a wata sabuwar hari da ‘yan hari da bindiga suka kai wa ofishin jami’an ‘yan sandan da ke yankin Afuze, karamar hukumar gabashin Owan, a Jihar Edo.
An kuma bayar da cewa an lallace kayaki da kuma kadamar da zubar jini a sakamakon harin.
6. Gidan Sama ya rushe kan ajin ‘yan makaranta a Jihar Legas
Rayuka da daman sun mutu sakamakon Gidan Saman mai taki ukku da ya rushe a shiyar Ita Faji, a nan birnin Legas a ranar Laraba (jiya), 13 ga watan Maris.
Abin ya faru ne misallin karfe goma na safiyar ranar Laraba da ta gabata, a yayin da gidan saman ya rushe daga sama har kasa inda ajin makarantar yara ta ke a kasar ginin.
7. Deji Adeyanju ya janye daga zanga-zangan ‘Our Mumu Don Do’
Dan zanga-zangan siyasa, Dan Sarki Deji Adeyanju a ranar Laraba da ta gabata, ya gabatar da janyewar sa daga hidimar zanga-zangan “Our Mumu Don Do” da sanannan dan Najeriya mai nishadarwa, Charly Boy ke jagoranta.
Deji ya gabatar ne da janyewar a layin nishadarwan sa ta twitter da zargin cewa Charly Boy ya ci amanan sa a lokacin da yake kulle a gidan Jaru.
8. Shugaba Muhammadu Buhari yayi bayani game da Gidan saman da ta rushe a Legas
A ranar Laraba da ta wuce, Shugaba Muhammadu Buhari yayi gaisuwar ta’aziyya ga iyalan yara da malaman makaranta da suka mutu, da kuma suka samu rauni sakamakon gidan sama da ta rushe kan wata makaranta a Jihar Legas. kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a baya.
Ginin mai taki ukku da ke a shiyar Ita Faji, a nan Jihar Legas ya fadi ne saman ajin ‘yan makaranta da ke kasar ginin a missalin karfe goma na safiyar ranar Laraba da ta wuce.
Ka samu cikkaken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa