Uncategorized
Kalli Jihohin da za a gudanar da Zaben ranar Asabar ta gaba
A ranar Alhamis, 21 ga watan Maris da ta gabata, Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) sun gabatar da Jihohin da za a gudanar da zaben kujerar Gwamnoni da wasu zabanni da aka dakatar a baya.
Kamar yadda hukumar ta sanar a baya da cewa zata kadamar da sauran zabannin a jihohin kasar a ranar 23 ga wata Maris 2019.
Sun gabatar ne a wata takarda da cewa zaben zai kasance ne a Jihohi biyar a kasar.
Kalli tsarin zaben a kasa;
JIHA HUKUMOMI
Bauchi Kananan Hukumomi 14
Benue Kananan Hukumomi 22
Plateau Kananan Hukumomi 9
Kano Kananan Hukumomi 29
Sokoto Kananan Hukumomi 22
Ko da shike Naija News Hausa ta gane da cewa akwai jayayya tsakanin Kotun Kara da Hukumar INEC game da zaben Jihar Bauchi. Mun kuma ruwaito a baya da cewa hukumar INEC ta gabatar da yadda zasu kadamar da zaben Jihar Bauchi.