Uncategorized
2019: Ifeanyi Ubah ya Koma ga Jam’iyyar APC
Sanatan da ke Wakilcin Jihar Anambra ta Kudu, Ifeanyi Ubah, yayi murabus da jam’iyyar sa na da, watau Jam’iyyar Matasa (YPP), ya koma ga Jam’iyyar APC.
An gabatar ne da komawar Ubah ga Jam’iyyar APC daga bakin ciyaman na hidimar neman zaben Jam’iyyar APC na tarayya, Adams Oshiomhole, a ranar Litini da ta gabata.
Oshiohmole ya bayyana a wata zaman tattaunawa da yayi da sabbin Sanatocin Jam’iyyar APC da tsohin sanatocin, da cewa Ifeanyi Ubah ya zama sabon mamban jam’iyyar APC.
Ko da shike Ubah bai bayyana a fili dalilin sa da janyewa daga jam’iyyar YPP ba, amma Oshiomhole, a cikin bayanin sa ya ce “Ubah dan siyasa ne mai wayo da hankali. Za kudura da shigar Jam’iyyar da ke shugabanci.”
Karanta wannan kuma: Wata Macce a Jihar Kaduna ta gudu da barin jaririn ta kulle cikin leda