Uncategorized
Ba ruwanku da yadda zamu tafiyar da shugabancin mu, APC ta gayawa PDP da Sanata Saraki
Jam’iyyar APC sun mayar da martani ga Jam’iyyar Adawa (PDP) da Sanata Bukola Saraki akan hidimar zaben shugaban gidan Majalisar Dattijai.
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa a Manyan Labarun Jaridun Najeriya ta ranar 2 ga watan Afrilu da cewa shugaban gidan Majalisar Dattijai, Sanata Bukola Saraki ya shawarci manyan shugabannan Jam’iyoyi da janye kansu daga zaben sabon shugaban gidan Majalisar Dattijai na tara.
“Ya kamata a bar ‘yan Majalisa su zabi wanda zai jagorance su ba tare da wasu manyan shugabannan Jam’iyya sun kafa bakin su ba” inji bayanin Sanata Saraki a wata gabatarwa ta ranar Litini da ta gabata.
Babban sakataren Tarayya na Jam’iyyar APC, Lanre Isa-Onilu ya mayar da martani game da zancen Sanata Saraki, Ya ce “Bai dace a bakin Jam’iyyar Adawa ba da bada shawara ko bayyana yadda jam’iyyar APC da ke kan shugabanci yadda zata kadamar da shugabancin ta ba”
“Jam’iyyar adawa ba zasu gaya mana yadda zamu kadamar da shugabancin mu ba. Su tsare tasu kujera, ba ruwansu da yadda muke tafiyar da shugabanci” inji Lanre.
Karanta wannan kuma: Kalli Shawarar da Sanata Saraki ya bayar ga ‘yan Gidan Majalisar Dattijai