Uncategorized
Kotun Kara ta bayar da dama ga PDP don binciken kayan hidimar zaben Jihar Kano
An bayar da dama ga Jam’iyyar adawa (PDP) ta Jihar Kano don kadamar da binciken ga kayaki da takardun da Hukumar INEC tayi amfani da ita wajen hidimar zaben kujerar Gwamna ta Jihar Kano da aka kamala a baya a ranar 9 ga watan Maris 2019.
Naija News Hausa ta gane da cewa dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Kano daga Jam’iyyar PDP da zaben 2019, Abba Kabiru-Yusuf na kalubalantar Hukumar INEC da gabatar da Abdullahi Ganduje daga Jam’iyyar APC a matsayin mai nasara ga tseren zaben Gwamnan Jihar Kano.
Kotun kara ta Jihar Kano, a jagorancin Alkali Halima Shamaki da Maliki Kuliya-Umar, ta bayar da dama ga Jam’iyyar Adawa, PDP don yin bincike ga takardu da kayakin da aka yi amfani da ita a wajen hidimar zaben.
Alkali Shamaki ya umurci Hukumar gudanar da hidimar zaben (INEC) da bayar da Fotokwafin takardu da kayakin da suka yi amfani da ita ga hidimar zaben Jihar ga Jam’iyyar PDP don su yi bincike kamar yadda suka bukata.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo yayi rantsuwa da cewa ba zai yi murabus da Jam’iyyar dimokradiyya, PDP ba.
“Lallai an ci amanar Jam’iyyar PDP a zaben kasa da aka gudanar ‘yan makonnai da suka gabata a Jihar Gombe, amma lokaci ba ta karya.” inji Dankwambo.
Dankwambo kara gabatar da cewa da shi, da sauran masoyan jam’iyyar dimokradiyya, PDP da suka ki janyewa daga Jam’iyyar PDP ba tun hidimar zaben jam’iyyar 2015, ba za su yi hakan ba a yanzu.