Labaran Najeriya
APC: Ba da gangan na ki bayyana ga Ziyarar Buhari ba a Legas – Tinubu
Shugaban Jam’iyyar APC na Tarayyar kasar Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, yayi bayani a ranar Alhamis da ta wuce da cewa ba wai na kauracewa ziyarar shugaba Muhammadu Buhari bane da gangan kamar yadda mutane ke zargin sa da hakan.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Legas don kadamar da wasu ayuka. Mun kuma gane da cewa Bola Tinubu bai samu kasancewa ba a wajen hidimar, duk da cewa Jihar shi ne Legas.
Ganin wannan ne ‘yan Najeriya ke jita-jita da zargin cewa watakila Bola Tinubu ya kauracewa hidimar ne don rama abin da shugaba Muhammadu Buhari yayi na rashin bayyana ga wata hidima da shi Tinubu yayi a lokacin da yake hidimar murna da kara ga shekaru 67 da haifuwa.
Ko da shike, Tunde Rahman, mai bada shawarwari ga Bola Tinubu, a bayanin sa da manema labaran Daily Independent, ya bayyana da cewa Tinubu bai samu kasancewa a hidimar ba ne don baya a kasar Najeriya lokacin da Buhari ya ziyarci Legas.
”Asiwaju Bola Tinubu ba ya a kasar Najeriya a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Legas don kadamarwa, shi yasa bai samu kasancewa ba a hidimar duka” inji Rahman.