Connect with us

Uncategorized

Yadda ‘Yan Hari da Makami suka kashe wani Tsoho Mai Shekaru 80 a Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Lahadi da ta gabata, wasu ‘yan hari da makamai sun hari kauyan Guzurawa da ke a karamar hukumar Safana a Jihar Katsina, inda suka kashe wani tsoho mai tsawon shekaru 80 da haifuwa da ke a unguwar Unguwa Duwa, a kauyan Guzurawa.

Bayan hakan an kara da cewa sun harbe wani Magidanci mai suna Bishir B. da ke da shekarun haifuwa 41. A halin yanzu an bayyana da cewa yana a wata asibiti inda ake bashi kulawar jiki.

SP Gambo Isah, Kakin yada yawun Jami’an tsaron Jihar Katsina ya bada tabbacin hakan ga manema labarai da cewa lallai haka ne abin ya faru.

Ya ci gaba da fadin cewa rukunin tsaron su ta ‘Operation Puff Adder’ sun tiga sun mamaye yankin da kauyukan da ke a shiyar don bincike da neman kame wadanda suka aiwatar da mugun kisan.

A bayanin shi, ya gabatar da cewa a halin yanzu, Kwamandan tsaron ‘yan sandan daya daga cikin rukunin tsaron Jihar ya koma zama a kauyan don tabbatar da kare rayukan al’umma da ke a shiyar duka.

Bisa yada aka bayar ga manema labarai, an bayyana da cewa ‘yan harin sun kai kimanin mutane Hamsin da suka hari kauyan a missalin karfe Bakwai na maraicen (7.17pm) ranar da harbe harben bindiga ko ta ina.

An iya bayyanawa da cewa rukunin tsaron ‘Operation Puff Adder’ sun yi ganawar wuta da ‘yan harin amma ba a samu nasara akan su ba.

A karshe dai maharan sun samu kone babura biyu da wata motar hawa a kauyan kami suka yi gudun hijira.