Connect with us

Uncategorized

Ramadan! Ramadan!! Ramadan!!! Ga Sanarwan Saudi Arabia game da Watan Ramadan

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Ramadan Kareem

Kotun Koli ta babban birnin Saudi Arabia, a ranar jiya Alhamis, 2 ga watan Mayu 2019 tayi kira ga dukan Musulunman kasa da kula da fitar Wata na Ramadan a maraicen ranar Asabar ta gaba, watau ranar 29 da Shaban, watau a Kalandar Umm Al-Qura, da ya bayyana ranar 4 ga watan Mayu a Kalandar Turai.

Sanarwan kamar yadda Kotun Saudi Arabia ta bayar na kamar haka;

“Duk wanda ya gane da fitar Watan Ramadan ta ganin Idanun sa ko ta Na’ura, ya yi kokarin bayyanar da hakan a duk wata Kotu da ke kusa da shi don yin rajistan tabbacin hakan, ko kuma ya sanar ga hukumomin yankin inda ya ga watar don bada tabbacin ganin watan.”

An kara a sanarwan da cewa idan har ba wanda ya samu ganin Watan Ramadan a ranar Asabar din nan, har ga cikar rana 30 da watan Shaban ke da ita da zai karshe ranar Lahadi, lallai ya kama da cewa za a fara azumi kenan ranar Litini ta gaba, bisa umarnin Annabi (S.A.W).

Naija News na da sanin cewa Watan Ramadan itace wata na Tara ga Kalandar Musulunci da ake gudunar da hidimar Azumi (SAWM) a dukan Duniya don bin umarnin  Quran, kamar yadda aka bayar ga Annabi Muhammad (S.A.W)

KARANTA WANNAN KUMA: Yafi Kyau a Aurar da ‘ya Macce ko ‘Da Namiji da kankanin Shekaru – Akashat Ny’mat