Uncategorized
Na Kudurta da yiwa ‘yar Yarinyar Fyaden Dole – Umar
Wani mutumi da aka bayyana da suna, Umar Bello daka shiyar Wurro-Chekke ta birnin Yola, a Jihar Adamawa, ya bayyana ga Kotun Kara dalilin da ya sa ya tashi yiwa wata ‘yar yarinya fyade.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa Umaru Bello na fuskantar wata kara ne a Kotu da zargin fyade da wata karamar yarinya mai shekara 5 ga haifuwa.
Umar ya bayyana a gaban Kotun Karar ta Yola a ranar Laraba da cewa lallai da gaske ne ya dauki matakin yi wa yarinyar fyade.
“Gaskiya ne, Na tafi da yarinyar a cikin daji da kudurin yi mata fyade, amma na zo na canza kuduri na, na kuma fasa ga yin hakan” inji Umar.
Umar ya roki Kotun da gafarta masa da matakin da ya dauka, ko da shike bai kai ga yin hakan ba.
Naija News Hausa ta samu sanin cewa Jami’an tsaro ne suka gabatar da karar Umar Bello tun ranar 24 ga watan Afrilu da ta gabata, da kotun Kara.
Hon Umaru Isah, Alkalin da ke Jagorancin karar Umar ya daga karar zuwa ranar 15 ga watan Mayu ta shekarar 2015, watau Laraba ta gaba, da kuma bada umarnin mayar da Umar a Jaru har ga ranar.
KARANTA WANNAN KUMA: #Ramadan; Kalli Abubuwan da ya Kamata kowani Musulmi ya Kaurace wa a Lokacin Ramadan