Uncategorized
Kalli Matar da aka Kame da Kokarin Shigar da Wiwi a Gidan Yari
Rukunin Fasaha ga Kame Masu Laifi na Hukumar Ma’aikatan gidan Yari na Najeriya (NPS), da ke a kurkuku na Kano sun katange da kuma kame wata Macce mai suna Rifkatu Anthony da aka gane da kokarin shiagar da mugan kayan maye da kwayoyi (Wiwi) dauri 39 a cikin kurkukun.
‘Yar Macen da ake tuhuma ta fito ne daga Badawa Quarters a Kano, ta kuma yi kokarin shiga Kurkukun da wayo don bayar da miyagun ƙwayoyi a kulle cikin leda da kwalaye don ba da su ga wadanda ke ɗaure a kurkukun.
Bayan tambayoyi da bincike da hukumar suka yi da ita, Rifkatu Anthony ta bayyana cewa bata da sanin kayan da take dauke da shi, da zargin cewa wani ne da ake cewa ThankGod ya bayar da shi gareta don samar da shi ga ‘yan gidan yarin.
Kwamturola Janar na Hukumar NPS ta Jihar Kano, Mista Magaji A Abdullah, ya ratabba da jinjina wa ma’aikatan hukumar da rashin raunana ga aikin su, Yaki da Mugan Halaye a Jiahr, da kuma nuna halin fasaha musanman ga iya gane da Rifkatu.
Janar Magaji ya ci gaba da karfafa ma’aikatan hukumar da ci gaba da tabbatar da tsaro ta kwaran gaske da kuma cika da kula wajen tsaron ‘yan gidan Jarun duka a kowane lokaci.
“Duk wani Ma’aikaci ko Ofisan hukumar da aka gane da kokarin kadamar da makirci, musanman wajen taimaka wa ‘yan gidan yari da miyagun kwayoyi, hukumar zata dakatar da shi daga aiki, zai kuma fuskanci shari’a” inji shi.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Jami’an tsaron Jihar Neja sun kame Wani barawo mai suna Mohammed Yakubu, da aka gane da sace-sacen mutane.
A bayanin Yakubu, “kungiyar mu kan sace Mata ne da ake zancen da Aurar da su, ko kuma wadda aka gama auren ta bada jimawa ba. Don mun tabbatar cewa Mijin ta ba zai yi jinkiri ba wajen biyan kudi don ya ceci ranta” inji shi.