Connect with us

Uncategorized

Gobarar Wuta ya kone shaguna da akalla kayar Miliyan Hamsin (N50m) a Gombe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahotanni da cewa a farkon sa’a ta ranar jiya Laraba, 19 ga watan Yuni 2019, gobarar ya kone shaguna 25 a Babban kasuwar Gombe.

Bisa bayanin wadanda suka gana da alamarin, sun bayar da cewa gobarar ta dauki tsawon sa’o’i hudu, a yayin wutan ya fara ci ne tun daga karfe 1:45 na safiyar ranar Laraba, ya kuma kone shaguna 25 kurmus.

Ciyaman na kungiyar ‘yan kasuwar, Alhaji Uba Abdullahi, ya shaidawa manema labarai da cewa, hadewar wayar wutar lantarki ne ke da alhakin gobarar, da cewa an gane da hakan ne bayan da aka mayar da wutan lantarke a kasuwar.

A bayanin Malam Abdullahi, ya gabatar da cewa akalla kayar da gobarar wutan yayi ya barna zasu kai Miliyoyi Naira Miliyan Hamsin (N50m).

A cewarsa, mafi yawancin abubuwan da gobarar yayi wa barna sun kunshi kayar masu sayar da kayan aikin filastik, shagon Teloli, da kuma masu sayar da fatan saniya da dabbobi.

“Muna da rashin dacewa da hanya mafi kyau ga shiga kasuwar, wanda ya sa ya zama da matsala ga masana’anta da masu sayen kaya wajen shiga da fitar kasuwar, musanman lokaci irin haka da gobara ya kone kasuwa” inji Abdullahi.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gobarar Wuta ya kame shaguna 200 a wata Kasuwa a Jihar Benue.

Ko da shike Misat James, wani masana’anci a kasuwar ya iya nuna da cewa ba wanda har yanzu ya gane da sanadiyar gobarar wutan, a fadinsa, an kule kasuwar ne tun karfe biyar da rabi na maraicen ranar, kuma babu wanda aka bari a ciki.