Connect with us

Uncategorized

Hukumar EFCC ta kame Barayin Layin Yanar Gizo (Yahoo Yahoo) a Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Bincike da Kare Tattalin Arzikin Najeriya (EFCC) ta sanar da kame masu sata a layin yanar gizo da aka fi sani da ‘YAHOO YAHOO’ bakwai (7) a wata unguwa mai layin lamba No.15, Giwa Road, Barnawa, a nan Jihar Kaduna.

Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai daga kakakin yada yawun hukumar, Mista Tony Orilade, ya bayyana da cewa barayin layin yanar gizon da suka kame ya kunshi Maza Shidda (6) da ‘Yar Mace Guda (1).

Ga sunayan su a kasa;

  1. Iyere Eromoseze Sylvester, Mai shekaru 40 ga haifuwa (Namiji)
  2. Uyiekpen Gabriel Etiosa, Mai shekaru 21 (Namiji)
  3. Elimia John, da shekaru 22 (Namiji)
  4. Eguasa Osas, da shekaru 24 (Namiji)
  5. Osaohian Osas, Mai shekaru 23 (Namiji)
  6. Faith Equasaogbomo, Mai shekaru 33, (Mace)
  7. Terry Ogbudu, Mai shekaru 25 ga haifuwa (Namiji)

Hukumar ta bada haske da cewa sun gane da katin tabbaci (ID Card) na wani ma’aikaci da dan Majalisar Wakilai, watau Mista Eromoseze Sylvester, a cikin kayakin da suka kwace a hannun barayin.

Haka kazalika suka sanar da gano wadannan kayaki da kayan arziki daga hannun barayin;

Motar Toyota Venza guda daya, Manyan wayoyin salula 18 hade da (iPhones, Samsung, a cikin su), Kwamfutar da ake yawo dashi (laptops) guda biyar, Katin tafiya zuwa kasar waje guda biyu, Layin wayar salula daban daban, Katin fitar da kudi a Banki (ATM goma sha daya), Agogon hannu masu tsadar gaske, Kayan Maye masu tsadar gaske da dai sauransu.

Hukumar ta bada tabbacin cewa ba zasu yi jinkiri da gabatar da su a kotu ba.

Naija News Hausa ta sanar a baya da cewa Jami’an tsaro sun kame wani tsoho a Jihar Bauchi da zargin yiwa karamar yarinya mai shekara 11 Fyaden dole.