Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 2 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 2 ga Watan Yuli, 2019
1. Atiku da PDP na shirye don bayar da shaidu 400 a Kotu
Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) da dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019, Atiku Abubakar, a ranar Litini da ta gabata, sun shaida wa Kotun Kara da cewa suna shirye don bayar da shaidu 400 da zasu bada tabbacin cewa Atiku ya lashe zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.
Jam’iyyar Adawar na da tsawon kwanaki 14 ne kawai don bada wannan tabbaci a kotu.
2. Hukumar NLC ta kalubalanci Gwamnatin Jiha da Gwamnatin Tarayya
Hukumar Ma’aikatan Najeriya (NLC) ta kalubalanci Gwamnatin Tarayya da ta Jiha da su karasa ga saurin biyan kankanin albashin Ma’aikata na naira dubu Talatin (N30,000) kamar yadda aka amince da ita a baya.
NLC ta gabatar da hakan ne a yayin da ma’aikatan kasar gaba daya ke jira tabbacin karban kudin kamar yadda gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta bada goyon baya da tabbacin biyan albashin ga ma’aikata bada jinkirta ba.
3. ‘Yan Hari da Bindiga sun kashe ‘Yan Sanda 4 hade da DPO
Naija News Hausa ta karbi rahoto da harin ‘yan ta’adda a Ofishin Jami’an tsaron da ke a Agudama, karamar hukumar Yenagoa, Jihar Bayelsa, inda suka kashe jami’an tsaro hudu da DPO guda.
Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, maharan sun sace makamai a Ofishin Jami’an tsaron, kamar Bindigogi da Kakin jami’an tsaron.
4. Kotu ta bada Umurnin ga Gwamnatin Tarayya da kwace kudi Dala $8.4million da N9.2 billion daga Matan Jonathan
Kotun Kolin Tarayya da ke a birnin Legas, a ranar Litini ta gargadi Gwamnatin Tarayya da Jiha da bada umarni ga Dame Patience, matan tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan da ta yardar da kudi mai kimanin dala Miliyan $8.4 da kuma Biliyan N9.2 ga Gwamnatin Tarayya.
Alkali Mojisola Olatoregun da ke jagorancin Kotun ta bayyana da cewa kudin da ke a asusun Patience kudin makirci ne da rashawa, a yayin da ba tabbacin cewa ta sami kudin ne wajen sana’a.
5. PDP ta kauracewa wata ganawa da Kwamitin NEC tare da Jam’iyoyi
Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), a ranar Litini da ta gabata ta kauracewa ganawa da Kwamitin NEC tayi da Jam’iyoyi, a jagorancin Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa (INEC).
Naija News ta fahimta da cewa zaman ganawar ya karbi halartar Jam’iyoyi 60, amma Jam’iyyar PDP ta ki halartan ganawar.
6. Fasto da ke Jagorancin Ikilisiyar COZA, Fatoyinbo ya janye daga matsayin sa
Babban Fastor da Jagoran Ikilisiyar Common Wealth of Zion Assembly (COZA), Fasto Biodun Fatoyinbo ya janye daga matsayin sa a jagoran Ikilisiyar.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa wannan ya faru ne bayan kara da zargi da Busola, wata shahararar mai daukar Hoto da kuma matan sananan Mawaki a kasar, Timi Dakolo, ta gabatar a wata Bidiyo da ya mamaye layin yanar gizo.
7. Atiku ya janye kwanaki Goma daka tsawon kwanaki da Hukuma ta bashi don gabatar da Shaidu
Jam’iyyar Adawa (PDP) da Atiku Abubakar sun amince da janye kwana 10 daga cikin kwanakin da Hukuma ta basu don gabatar da shaidu ga zargin makirci ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben watan Fabrairu da ta gabata.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne ga Kotun Kara a ranar Litini da ta gabata.
8. IGP Adamu ya bada umarnin a kamo ‘yan hari da makami da suka kashe DPO a Jihar Bayelsa
Babban Jami’in ‘Yan Sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu a ranar Litini da ta wuce ya yada yawu ga harin da wasu ‘yan harin da bindiga suka kai a Jihar Bayelsa, inda suka kashe Jami’an tsaro hudu hade da DPO da je wakilcin tsaron yankin Yenagoa.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan ta’adda sun hari Ofishin Jami’an tsaron da ke a Agudama, karamar hukumar Yenagoa, Jihar Bayelsa, inda suka kashe jami’an tsaro hudu da DPO guda.
9. EFCC ta bayyana lokacin da zata gabatar da Saraki a Kotu
Hukumar Kare Tattalin Arziki da yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya, EFCC ta bayyana lokacin da zata gabatar da Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai, Bukola Saraki a Kotu, akan wata zargin cin Hanci da Rashawa.4
Naija News Hausa ta fahimta da cewa hukumar na zargin Saraki ne da cin hanci da rashawa wajen sace kudin Jihar Kwara tsakanin shekarar 2003 zuwa 2011, a lokacin da yake zaman Gwamnan Jihar.
Ka samu Kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com