Labaran Najeriya
Oshiomhole: Jam’iyyar APC ta nada jagoran rukunin Babban Majalisa a Majalisar Wakilai
Ciyaman Tarayyar Jam’iyyar shugabancin kasa (APC) Adams Oshiomhole, ya bayyana da cewa jam’iyyar shugabancin kasar ta gabatar da Hon. Alhassan Doguwa a matsayin jagoran Majalisa ta sama a gidan Majalisar Wakilai.
Naija News Hausa ta sami tabbacin sanarwan ne kamar yadda tsohon gwamnan Jihar Edo ya sanar a wata ziyarar godiya da Doguwa tare da masu wakilci a Jihar Kano a jagorancin mataimakin gwamnan Jihar, Farfesa Hafizu Abubakar, suka kai ga Kwamitin Kadamarwa ta Jam’iyyar APC, a ranar Litini da ta wuce a birnin Tarayya, Abuja.
Naija News ta fahimta da cewa Doguwa, watau Sanata da ke wakilcin yankin Tudunwada/Doguwa a Majalisar Tarayya, ya samu tagomashi ne daga Jam’iyyar APC da kuma goyon bayan gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
A yayin da Oshiomhole ke bayani a ganawar, ya bayyana da cewa Jihar Kano ta bayar da yawar kuri’a fiye da sauran Jiha ga zaben shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa ta watan Fabrairu.