Labaran Najeriya
Abin da ya sa muka wa Shugaba Buhari tsuwa – Kingley Chinda
Bayani da ga wani dan Majalisar Wakilai a kan dalilin da ya sa suka wa shugaba Buhari tsuwa
Daya cikin yan Majalisar wakilai mai suna Kingsley Chinda daga Jam’iyyar PDP a Jihar Rivers ya bayyana dalilin su da ya sa suka yi wa shugaban kasan tsuwa a yayin da yake bada Kasafin kudi ga Majalisar a ranar Laraba.
Ya ce, Shugaban kasar bai nuna halin gaskiya da kuma imani ba ga ‘yan Najeriya a musanman idan a zo ga kasafin kudi, lokatai da dama ana anfani da wannan wajen zargen yan Majalisa ganin su ke da laifi. ya bada wannan ne ga yan jaridun Premium Times.
“A bin missali, yanzu a yau ya bayyana ga jama’a cewa akwai kimanin naira biliyan dari takwas (N800b) na kashe-kashen musanman, wanda ya banbanta ga Kashe-kashen musanman da ake da ita kasa mai kimanin naira tiriliyan shidda da hudu (N6.4tr). idan kun yi la’akari da wannan lissafin zai baku kashi goma sha shidda (16%) ga kashi dari.
inji shi, Abin nufi a nan shi ne cewa sun samar da kashi 16 ne kawai cikin kashi dari ga kashe-kashen kudi ta musanman. ta dalilin wannan kuwa tattalin arzikin kasar ba zai motsa.
A kashin gaskiya, ba wai mun shirya wannan tsuwa da zanga-zangar ba ne. mutane sun dubi wannan ne kamar mun shirya ta a haka.
Kuma in tabbatas maku, ba yan PDP kawai ne wannan kasafin ta zafa ba, har ma da yan Jam’iyyar APC. amma da yake suna Jam’iyya daya da shugaban, shi yassa basu samu karfin iya magana ko tsuwa ba.
Naija News ta ruwaito Abin takaici, ana ma Shugaba Muhammadu Buhari tsuwa a yayin da yake bada kasafin kudi na shekara ta 2019.