Connect with us

Labaran Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da Hutun Sallar Eid-il-Kabir

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta sanar da bada hutun Sallar Eid-il-Kabir.

Hutun bisa sanarwan da aka bayar a layin yanar gizo ta Twitter ta shugaban zai fara ne daga ranar Litini, 12 ga watan Agusta zuwa ranar Talata, 13 ga watan Agusta 2019.

Naija News Hausa ta samu tabbacin sanarwan ne kamar yada aka bayar da shi daga hannun Babban Sakataren Harkokin Kasa, Malama Georgina Ehuriah, a ranar Talata da ta gabata.

Georgina a yayin sanarwan ta gargadi al’umar Najeriya da janyewa daga duk wata halin tashin hankali, da kuma mara wa Gwamnatin Tarayya baya wajen samar da zaman lafiya da hadin kai a kasar Najeriya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnatin Saudiyya ta sanar da ranar 10 ga watan Agusta a matsayin ranar hawan Arafat, a wata sanarwa da aka fitar daga hannun Jamiu Dosunmu, na Sashin Harkokin Jama’a na Hukumar Kula da Mahajjata ta Amir-ul Hajj, Jihar Legas, Dr. AbdulHakeem Abdul-Lateef, a ranar Juma’a da ta gabata a Gidan Gwamnatin Jihar Legas da ke Makkah.