Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 9 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 9 ga Watan Agusta, 2019
1. Kotu ta Umarci EFCC da ta Kama Tsohon Shugaban INEC, Maurice Iwu
Babbar Kotun Tarayya da ke a Jihar Legas ta umarci Hukumar Yaki Cin Hanci da Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) da ta tsare tsohon Shugaban Hukumar gudanar da Zabe a Najeriya, Farfesa Maurice Iwu, har zuwa ranar Juma’a don sauraron karar tasa.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa a ranar Alhamis da ta gabata ne hukumar ta gurfanar da tsohon Shugaban Hukumar INEC bisa zargin ake da shi na karkatar da sama da Naira Biliyan 1.
2. Jam’iyyar APC ta Jihar Kogi ta Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Simon Achuba
Mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba ya samu dakatarwa daga sashin jam’iyyar APC ta Jihar.
Naija News ta fahimci cewa Achuba, mataimakin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bai sami kyakkyawar alakar aiki tare da shugaban sa ba tun da aka zabe su tare.
3. Bazaka Iya Amfani da Cin Hanci ba Don Yaki da Cin Hanci da rashawa – Lauyan ya gayawa shugaba Buhari
Inibehe Effiong, daya daga cikin lauyoyin da ke neman a saki Omoyele Sowore, dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga tsare a hannun Jami’an tsaro don wata hidimar Zanga-Zanga.
Effiong ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da kin sauraren kukan ‘yan Najeriyar “duk da amfani da kudin masu biyar haraji don magance kamuwa da cutar kunne da yake da shi, a kasar Turai.”
4. Shugaba Buhari ya mayarda martani ga kisan jami’ai a jihar Taraba
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya umarci hedikwatar tsaron kasar da ta fara gudanar da bincike ta musanman da hanzari game da kisan jami’an ‘yan sanda uku da wani mutumi da sojoji suka kashe a Jihar Taraba.
Naija News Hausa ta sami tabbacin umarnin Buhari ne a wata rahoto da aka bayar daga hannun Babban Hafsan Hafsoshin na Sojojin Sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ga manema labarai, bayan wata ganawa da shugaba Buhari ya jagoranta.
5. Gidan Majalisar Wakilai ta Mayar da Martani ga hukuncin Kotu akan Majalisar Jihar Edo
Majalisar wakilai ta yi Allah wadai da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta bayar na hana Majalisar Dokoki da daukan mataki akan hidimar Majalisar Wakilai ta Jihar Edo.
Ka tuna cewa kotu ta hana Magatakardan Majalisar Dattijai, shugaban majalisar dattijai da kuma kakakin majalisar wakilai damar karbe ikon majalisar wakilan jihar Edo.
6. Ku gayawa Al’umar Najeriya inda Alhaji Hamisu yake – ‘Yan Sanda sun kalubalanci Rundunar Sojoji
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tuhumi hukumomin Sojojin Najeriya da su bayyana inda sanannen dan fashin nan, Alhaji Hamisu Bala Wadume yake.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa ‘Yan Sanda sun furta hakan ne ga Sojojin Najeriya bayan ganin yadda aka kashe jami’an tsaron su guda Uku a Taraba da barin mugun Dan Fashin da gujewa.
7. Shugaba Buhari Ya kara Ganawa Da Shugabannin Tsaro A Abuja
A ranar Alhamis din da ta gabata, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da shugabannin ma’aikatu inda aka yi masa jawabai kan yanayin rashin cikakken tsaro da ake fuskanta a kasar.
Bisa ganewar Naija News, ganawar ta fara ne a ofishin shugaban kasa a fadar gwamnatin da misalin karfe 10:30 na safiyar yau.
Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa