Connect with us

Uncategorized

Jami’an Tsaro sun kame wasu da Kudi Marasa Kyau a Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Tsaro ta Jihar Kano sun kame wasu mutane Biyar da Laifin Kira da amfani da Kudaden Najeriya da ta kasan Waje mara sa kyau.

Naija News Hausa ta sami tabbacin hakan ne bisa bayanin Kwamishanan Jami’an Tsaron jihar, CP Ahmed Iliyasu, ga manema labarai a bayan da rukunin tsaro ta Operation Puff Adder suka kama mutanen.

Ya bayyana da cewa rukunin tsaron ta Operation Puff Adder sun ci karo ne a ranar 6 ga watan Agusta 2019 da mutanen.

Sunayan su na kamar haka; Saidu Sarki mai shekaru 35 da haifuwa da kuma Ubale Saleh mai shekaru 50.

“Rukunin tsaro ta Operation Puff Adder na Anti-Daba Kano ne suka tari mutanen da tarin kudin kasar Faransi CFA 10,000 da kuma Dala 105 ta kudin U.S, hukumar tsaro kuwa na kan bincike da wannan” inji Shi.

A haka kuma rundunar tsaron suka kame wasu kuma a Maiduguri, Jihar Borno da tarin Daloli mara sa kyau a ranar 10 ga watan Agusta 2019 a nan shiyar Badawa ta Jihar. A inda suka iske tarin Daloli mai dauri 178 na Naira Dari-dari ta kudin U.S, da kuma tarin kudin Najeriya a kashi goma ga Dauri.

Inji shi “A ranar 10 ga watan Agusta 2019, a misalin karfe Bakwai na Maraice, rukunin tsaro ta Operation Puff Adder da hadin kan Hukumar SARS sun kame wasu masu suna kamar haka, Goni Mustapha,  Alh Ali Goni da kuma Hassan Goni dukansu daga Maiduguri, a hanyar Sabon Garin Kano, suka kuwa kwace Daurin Kudin Dala mara Kyau 48, da kuma Kwamfuta”

KARANTA WANNAN KUMA; Shaidan ne ya shige ni – inji Mutumin da aka kama da laifin Jima’i da Almajirai 32 a Kontagora, jihar Neja