Connect with us

Uncategorized

An Kashe ‘Yan Shi’a Uku a Jihar Kaduna

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rahoton da ta isa ga Naija News Hausa a yanzun nan na bayyana da cewa an kashe ‘yan kungiyar ci gaban hidimar adinin musulunci a Najeriya (IMN) da aka fi sani da suna ‘Yan Shi’a Uku a garin Kaduna.

Abin ya faru ne a yau, safiyar ranar Talata 10 ga watan Satumba 2019 a kan hanyar Bakin Ruwa, wata unguwa a Jihar Kaduna, a inda aka kashe ‘yan kungiyar IMN Uku ta hannun Jami’an tsaron Jihar a lokacin da ake hidimar Ashura.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya  (IGP), Mohammed Adamu, a karshen makon da ta gabata, ya ba da umarnin ga dukan rukunin ‘yan sanda a duk fadin kasar da su fara kame shugabannin kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), da aka fi sani da Shi’a.

Ko da shike kakakin yada yawun Jami’an Tsaron Jihar, DSP Yakubu Sabo ya yi watsi da rahoton, da fadin cewa ba gaskiya ba ne.