Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini 30 ga Watan Satumba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 30 ga Watan Satumba, 2019
1. Gwamnatin Shugaba Buhari Na Shirin Karar Alkalin da ya yanka Hukunci Sakin Sowore
Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na shirin kai karar Alkali, Mai shari’a Taiwo Taiwo ga Majalisar Shari’a ta kasa (NLC) don bayar da belin da ya yi ga Omoyele Sowore, jagoran zanga-zangar #RevolutionNow.
Naija News ta tuna da cewa Babban Kotun Tarayya da ke Abuja karkashin jagorancin Mai shari’a Taiwo ta bayar da Beli ga Sowore wanda ake tuhuma da laifin shirin tayar da tashin hankali a kasa.
2. ‘Yan sanda sun Tabbatar da Karban Yancin Mahaifiyar Samson Siasia
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta reshen jihar Bayelsa ta tabbatar da cewa Madam Beauty Ogere, mahaifiyar Samson Siasia, tsohon kocin ‘yan wasan Super Eagles, ta samu yanci daga hannun ‘yan Garkuwa.
Don bada tabbacin hakan, a ranar Lahadi Mista Asinim Butswat, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Sufeto Janar na ‘yan sandan yankin, ya ce rundunar ‘yan sanda za ta fitar da sanarwa ta musanman game da hakan ba da jimawa ba.
3. Gwamna Wike ya Tsoratar da PDP, APC Akan rijiyoyin Mai
Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Enzo Wike ya gargadi sauran jihohi da karban rijiyoyin mai da ba bisa ka’ida ba na jihar.
Ya yi wannan gargadin ne yayin da yake zantawa wajen hidimar kadamar da Hanyar Birabi Street, Elegbam-Rumueme a karamar hukumar Obio / Akpor ranar Juma’a.
4. Tunde Bakare Ya Bayar da Sabon Bayani game da Karbar Muki bayan Shugaba Buhari
Babban Fasto da Janar Overseer ta Ikilisiyar Latter Rain Assembly, a jihar Legas, Fasto Tunde Bakare, ya ce faifan bidiyon da ya mamaye layin yanar gizo inda ya yi barazanar zama shugaban kasa, ya yi hakan ne kawai don bayyana burin sa.
Naija News ta tuno da cewa malamin ya shelanta a cikin wata Bidiyo da cewa zai karbi mulki daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da wa’adinsa ya kare a shekarar 2023.
5. ‘Yan Sanda Sun Mayar da Martani akan Harin Banki a Abia
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta reshen jihar Abia ta bayyana wani shirin da wasu gungun ‘yan fashi da makami yi don kai hari kan cibiyoyin ajiyar Kudade a Aba, babban birnin jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron jihar (PPRO), SP Geoffrey Ogbonna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da manema labarai ranar Lahadi, a madadin Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ene Okon.
6. DSS sun Kama wani Dan Yaki da Yancin Bil’Adama, Chido Onumah
Hukumar Tsaron Jiha-da-Jiha (DSS) sun kame wani Dan Yaki da Yancin Bil’Adama a Najeriya, Chido Onumah.
Naija News ta fahimta da cewa an kama mai yada labarai Onumah ne, a Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe yayin da yake dawowa daga Barcelona, Spain, inda ya kamala karatun digiri ga Sadarwa.
7. Shugabancin kasa ta Mayar da Martani ga Rashin Kasancewar Aisha Buhari daga Aso Villa
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin da ke cewa matar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha, ta fita daga kasar zuwa kasar waje saboda takaddama da ke afkuwa a fadar Shugaban kasa.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Uwargidan Shugaban kasar ta fice daga kasar nan kusan watanni biyu a yanzu, a sanadiyar rikicin da ke afkuwa a Aso Rock.
8. #RevolutionNow: Gwamnatin Tarayya da sanar da ranar sake Kame Sowore
Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta sanya ranar Litinin, 30 ga Satumba, don gurfanar da jagoran zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, a gaban babbar kotun tarayya, Abuja.
Naija News ta tuna da cewa Gwamnatin Tarayya ta shigar da kararrakin da suka shafi hada baki da cin amanar kasa da kuma karkatar da wasu kudade a kan mawallafin SaharaReporters.
9. Shugaba Buhari Ya Tsige Shugaban Kotun Daukaka Karar Shugaban Kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da korar Siaka Isiah Idoko-Akoh, Shugaban Kotun Shari’a Kan Zubar Jari da Tsaye.
Naija News ta samu tabbacin rahoton ne a wata sanarwa da sakataren din-din din na ma’aikatar kudi ta tarayya, Dr. Mahmoud Isa-Dutse ya fitar.
Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya ta kullum a shafin Naija News Hausa