Labaran Najeriya
‘Yan Sanda Sun Gano Da Wata Cibiyar Azabtarwa A Cikin Daura, garin shugaba Buhari
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ci karo da wata Cibiyar Azabtarwa ta addinin Musulunci ’a Nassarawa Quarters, Sabon Gari, Daura, garin shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.
Naija News ta fahimci cewa wannan ya biyo ne bayan makwanni biyu da aka ci karo da irin wannan a yayin binciken da aka yi a Kaduna, inda aka gano ‘yan fursuna da aka tsare.
A cewar rahoton kamar yadda manema labarai suka bayar, an gano ginin ne bayan da wasu yaran da suka tsere daga wajen suka shiga zanga-zangar rashin amincewa da cin zarafin bil-adama da ke gudana a cibiyar mallakar wani fitaccen malamin addinin Musulunci da ke a Daura, wanda aka bayyana sunan sa da Bello Mai Almajirai.
A bayar da cewa Cibiyar an kafa shi ne don wadanda suka yi rashin ji ko biyayya ga iyayensu ko kuma al’umma.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Sanusi Buba, ya ba da bayanai ga ’yan jarida a cibiyar ranar Litinin da ta wuce da cewa Malam Bello ya kwashe shekaru 40 a gudanar da cibiyar sannan daga baya sai ya barwa dansa, Umar Bello, jagorancin wajen.
Ya koka kan irin ayuka da halin da ke gudana a cikin cibiyar, ya kara da cewa kowane ɗayan dakuna shida da ke a wajen ya daukan yawar mutane 40 ne, a kuma tattarasu a dakin da barin su da aiwatar da ayukan kazanta muni.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa kimanin mutane 300, hade da manya da yara daban-daban daga kasashe makwabta ne aka kubutar da su daga wajen.
Kalli wasu hotuna da aka dauka a wajen;