Labaran Najeriya
2023: Yadda Za a Hana Wa’adin Buhari na Uku – Matasan Arewa
Shugaban kungiyar Arewa Youths Consultative Forum (AYCF), Yerima Shettima, ya yi kakkausar suka kan duk wani yunƙuri na tsawaita wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa 2023.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ruwaito a baya da rahoton cewa, wasu gungun jama’a sun yi kira ga Shugaba Buhari da ya tsawaita wa’adin shugabancinsa zuwa shekara hudu bayan wannan wa’adin.
Haka kazalika, lauyan kundin tsarin mulki da yaki da yancin bil adama, Femi Falana (SAN) ya zargi Shugaba Buhari da shirya makircin wa’adi na uku a 2023.
Femi Falana ya bayyana matakin da Buhari da mutanensa ke yi na kara tsawon jagorancin shugaban a kasar bayan wannan wa’adi da ake a ciki.
A wata hirar da Shettima ya yi da manema labaran kamfanin dilancin labarai ta Daily Post, ya yi gargadin cewa za a watsar da matasan Arewa don tabbatar da dakatar da wannan yunkuri da gwamnatin a yanzu ke kokarin gabatarwa na wa’adi na uku.
“duk wani yunkuri na ci gaba da mulkin Buhari, zai sha kaye ne kamar irin ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo,” inji Shettima.
“Muna sane da cewa wasu abubuwa na gudana a cikin wannan gwamnatin. Muna sane da cewa batun shirin wa’adi na uku na ci gaba a kasa amma gwamnati ba ta fito fili ta bayyana wannan shiri ba, ko kuma su yi rashin amincewa da zargin haka,”
“Jita-jita game da wa’adi na uku na yaduwa a ko’ina kuma zai mutu kurmus kamar shirin wa’adi na uku da Obasanjo ya nema, domin mun ƙuduri aniyar mu da kuma tabbatar da cewa batun wa’adi na uku bai ga hasken ranar ba a kasar.” inji Shettima.