Uncategorized
Jam’iyyar PDP Sun Yi Allah Wadai da Dokar Kisa ga Masu Yada kalaman Kiyayya da Majalisar ta Shirya da Yi
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tayi Allah wadai da kudirin da majalisar dokoki ke gabatarwa na kudurin kisa ta hanyar rataye ga masu yada kalaman kiyayya, wadda Sanata Sabi Abdullahi ya gabatar.
Naija News ta fahimci cewa an karanta kudirin ne a karo ta farko a gaban majalisar ranar Talata da ta gabata.
PDP a yayin mayar da martani game da zancen a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ta hannun sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Kola Ologbondiyan ya bayyana kudirin a matsayin dokar cin mutunci, mugunta da kisa.
Jam’iyyar ta ce ana shirin zartar da kudirin ne don dakile muryoyin da ke yin adawa da hukuncin All Progressives Congress (APC).
A cewar PDP, Dokar Kiyayyar ta sabawa dokar kasa, wacce ba ta bin doka da oda ba .
“Jam’iyyarmu tana da ra’ayin cewa, idan har an tabbatar da wannan dokar kisan masu kalaman kiyayyar, lallai zai raunana tsarin mulki da dokokin kasar, zai lalata tsarin dimokiradiyyarmu, da kuma dakile ‘yancin’ yan kasa da kuma haifar da mummunan son kai a Najeriya.”
KARANTA WANNAN KUMA; Idan ba za ku iya ciyar da Iyalanku ba, to kada ku tura yaranku don yin bara a Madadin ku – inji Sarkin Kano