Labaran Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Zata Dauki Bashin Miliyan 500m (Euros) Don Kirar Ayyuka Da Masana’antu
Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) ta amince da tsare-tsaren gwamnatin tarayyar Najeriya na karbo bashin Euro miliyan 500.
Wannan shirin ya bayyana ne daga bakin Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Clement Agba, a karshen taron FEC da ya gudana a ranar Laraba a Abuja wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Bisa ga bayaninsa, za a yi amfani da rancen ne don tallafawa masana’antu, samar da ayyukan yi, da kuma aikin gona kuma ana tsammanin zai samar da guraben ayyuka miliyan 1.2 a kasar.
A ganewar Naija News, Bankin Masana’antu na Kasa (BOI) ne zata jagorancin tsarin rabas da kudin.
“A yau ne majalisa ta amince da samar da garanti na Mai kudin Yuro miliyan 500 daga reshe na Credit Suisse AG London, da damar tsayuwar masu ba da lamuni na duniya don tsayawa rancen kudin na Euro miliyan 500 ga Bankin Masana’antu.”
“Bashin dai za a karbe shi ne don tallafawa manyan ayyukan masana’antu da kuma kananan kamfanoni da matsakaitan masana’antu da ke darajar silsila a Najeriya har na tsawon shekaru biyar kan farashi mai sauki.”
“Gwamnatin Tarayyar Najeriya ne zata kasance da tsayuwa ga rancen, kuma za a tafiyar da tsarin kashe kudin ne ta hannun Ma’aikatar Kasafin Kudi da Tsarin Kasa.”
Gwamna Jihar Kogi, Yahaya Bello a wata sanarwa da Naija News Hausa ta bayar a baya, ya karyata rahoton da ke cewa ana bin sa bashin albashin ma’aikata a Jihar Kogi, ya lura cewa irin wannan rahoton karya ne.
Gwamnan jihar Kogi ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta gamu da alawus din ma’aikatan da ke jihar kuma ya nace cewa gwamnatinsa ba ta bin ma’aikata bashin ko taro.