Labaran Najeriya
Shugaba Buhari Ya Gabatar Da Nadin Sabon Ciyaman Na AMCON
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Mista Edward Adamu a matsayin Shugaban Kamfanin Kula da Bada da Talla na Najeriya, watau ‘Asset Management Corporation of Nigeria’.
Kamfanin Dilancin Labarai ta Naija News ta fahimci cewa wannan sanarwan ya fito ne a kunshe a cikin wata wasika da shugaban kasar ya aika wa Majalisar Dattawa a safiyar yau.
Wannan gidan labarai ta mu ta kula da cewa nadin Edward ya biyo ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da tsige Mista Muiz Banire a matsayin Shugaban Hukumar (AMCON).
‘Yan awanni kasa da 24 da Buhari ya kuma ba da sanarwar maye gurbin shugaban FIRS, Fowler da wani dan Arewa, matakin da ‘yan Najeriya suka yi sokaci da ita.
Ko da shike shugaba Buhari ya rubuta wasika ga majalisar dattijai don neman alfarma da tabbatar da sabon shugaban na AMCON da ya gabatar.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Gwamnan Adamawa, Fintiri Ya Hana Ciyamomin Kananan Hukumomi Tafiye-Tafiye
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya gargadi shugabannin kananan hukumomi a jihar daga tafiye-tafiyen da basu kamata ba. Gwamnan na mai cewa gwamnatin sa “ba za ta amince da irin wannan dabi’a ba inda shugaba zai yi watsi da aikin jami’in nasa ba tare da dalili ba.”
Fintiri ya tuhumi sabbin shugabannin da aka nada da samar da rabon dimokiradiyya ga jama’arsu tare da hana su tafiye-tafiye marasa galihu daga kananan hukumominsu, sai dai idan tafiyar ya zama dole.