Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 12 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 12 ga Watan Disamba, 2019
1. Aisha Buhari ta aika da Gargadi mai karfi ga Garba Shehu da Mamman Daura
Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta aika da sakon kalubalanta da zargi ga Mamman Daura, dan uwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da cewa yana bada umarni ba tare da yardar Shugaban kasar ba.
Naija News Hausa ta gane da cewa rashin jituwa tsakanin uwargidan shugaban kasar da dangin Mamman Daura ya bayyana ne a fili a watan Oktoba bayan da Aisha ta dawo daga tafiyarta a Turai.
2. Ma’aikatan Wutar Lantarki Sun Dakatar Da Yunkurin Yajin Aiki
Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa (NUEE) ta dakatar da yunkurin yajin aiki da suka fara, ‘yan sa’o’i bayan da fadin kasar ta fuskanci rashin wutan Lantarki bisa mataki da ma’aikatar wutan lantarki ta kasar suka dauka.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Ma’aikatan Wutar Lantarki sun dakatar da yajin aikin ne bayan wani taro da wakilan Gwamnatin Tarayya suka yi a daren Laraba.
3. Kamfanin Dilanci Labarai ta Punch Ta Kalubalanci Shugaba Buhari, Da Alkawarin Kiransa Janara
Wani babban gidan watsa labarai a Najeriya, Punch ta yi taka-tsantsan kan tsarin shugabancin Muhammadu Buhari, Shugaban kasar Najeriya.
Gidan jaridar a cikin sanarwar da ta wallafa a ranar Laraba, ta zargi gwamnatin Shugaba-Buhari da nuna rashin biyayya ga ‘yancin bil adama da kuma keta duk wasu makaman gwamnati da cibiyoyin dimokiradiyyar kasar.’
4. Kotun ECOWAS ta Ba da hukuncin Karshe kan karar da Nnamdi Kanu ya yi wa Gwamnatin Najeriya
Kotun Kolin ta ECOWAS ta yi watsi da karar da Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) ya yi wa Gwamnatin Najeriya, bisa zarginsa da azabtar da shi, cin zarafin sa da yi masa tsananci ta hannun jami’an tsaro a lokacin da aka kama shi a shekarar 2015.
Naija News ta ruwaito bisa wata rahoto da jaridar Vanguard ta bayar, ta ce Kotun ECOWAS a cikin hukuncin da Mai Shari’a Dupe Atoki ta bayar, ta ce shugaban IPOB din ya gaza tabbatar da zargin da ya yi wa Gwamnatin Najeriya.
5. Akpabio Ya Janye Daga Makomar Zaben Sanatocin a Neja Delta, Ya kuwa bada Dalilai
Ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya fice daga makomar zaben majalisar dattijai na wakilcin Arewa maso yamma ta Akwa Ibom da za a yi a watan Janairu.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa Ministan ya sanar da matakin nasa ne a wata wasika da ya aika wa Shugaban tarayyar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole.
6. Ba Mu Gama Da Siyasa Ba Tukunna, Muna Nan Dawo Wa A Shekarar 2023 – Shehu Sani
Tsohon Sanata da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani a ranar Laraba ya yi alfahari da cewa bai janye daga siyasa, yana nan dawo nan da shekarar 2023.
Shehu ya bayyana hakan ne a gidansa da ke Kaduna lokacin da kungiyar Magabata na Sabon Garin Nassarawa suka ba shi wata kyautar lambar yabo don kyakyawan aikinsa da kuma halin karimci ga wakilcin al’umma.
7. Rundunar Sojojin Sama Ta Kadamar Da Operation Rattle Snake
Rundunar Sojan Sama ta Najeriya, a karkashin rukunin yaki ta soja da aka fi sani da Operation LAFIYA DOLE, ta kaddamar da sabon rukunin mai taken “Operation Rattle Snake” don yaki da ta’addanci da ke gudana a yankin Arewa maso Gabas.
Air Commodore Ibikunle Daramola, Daraktan hulda da jama’a na hukumar NAF ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba da ta wuce a Abuja.
9. Kai ɗan haya ne A Aso Rock – Emelieze Ya Gayawa Buhari
Shugaban kungiyar Dukkan Ma’aikata, Andrew Emelieze ya kalubalanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da cewa ya tuna cewa shi dan haya ne a Aso Rock.
Tsohon shugaban kwamitin kungiyar kwadagon ta Najeriya, reshen jihar Oyo, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Ibadan, babban birnin jihar.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau a Naija News Hausa