Labaran Najeriya
Aisha Buhari ta gargadi Mata da Matasa don jefa zaben su ga Buhari a zaben 2019
Matar Shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari ta bukaci Mata da Matasa su sake zaben Shugaba Muhammadu Buhari a zabe na gaba.
“Ina da murna da kuma gaba gadin fadin nuna goyon baya na ga Jam’iyyar APC ganin irin cin gaba da aka samar a kasar da ire-iren aiki da shugabanci ta samar ga al’umma”. in ji Aisha Buhari.
Aisha Buhari ta kara da cewa, a shekara ta 2015, Jam’iyyar APC ta yi wasu alkawalai; kuma ina da farin cikin cewa Jam’iyyar ta cika cikin alkawalan da dama ga jama’ar Najeriya.
Matan Shugaban ta yi wannan kira ne a wajen shirin bude filin rali ta Jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Kano, a nan Filin wasan Kwallo ta Sani Abacha da ke Kofar Mata, a Jihar Kano.
Naija News ta ruwaito a baya akan Manyan Labarai na Jaridun Najeriya ta ranar 24 ga Watan Disamba ta shekarar 2018 cewa Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi amfani da Godswill Akpabio International Stadium da ke a birnin Uyo ba, don shirin neman zabe na shekarar 2019.
Duk da hakan tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Sen. Godswill Akpabio ya ba da tabbacin cewa zai yi iyakan kokarin sa da ganin cewa Jihar na sa ta jefa kuri’ar su ga Jam’iyyar APC a zaben 2019 da ke gaba.
Ya kara da cewa abin fahari ne da ganin cewa Jam’iyyar ta kadamar da shiri masu kyau da gaske da har Matasan Najeriya sun sami damar shiga don samun hanyar cin abin ci da kuma hanyar zamantakewa da fita cikin zaman tasha ko ta’addanci.
Cikin wadanan shiri aka sami: N-Power, bada Abinci ga ‘Yan Makarantan Sak
andari, Bada tallafin kudi ga ‘yan kasuwa, da de sauran su.
Akpabio ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari da cewa Jam’iyyar APC ta Jihar Akwa Ibom za ta yi iya kokarin ta don jawo hankalin Matan Jihar ga ganin cewa sun jefa kuri’ar su ga shugab Muhammadu Buhari a zabe na gaba.
Karanta kuma: Babban Shugaban kungiyar Miyetti Allah a Jihar Benue, Alhaji Garus Gololo ya bayyana ce wa idan har ‘yan Najeriya suka goyawa Atiku baya har ya hau ga shugabanci, lallai zai raba kasar biyu.