Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 17 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 17 ga Watan Disamba, 2019
1. Rundunar Sojojin Najeriya Sun Sarwake Major Janar 20, Brigadier Janar 10
Rundunar Sojojin Najeriya sun sake girke Manjo-janar 20 da Birgediya-Janar 10 a cikin abin da ake gani a zaman babban koma-baya a rundunar.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Sojojin Najeriya sun ba da sanarwar sake daukar manyan hafsoshin sojojin ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, 16 ga Disamba ta hannun Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kanal Sagir Musa.
2. Boko Haram: Leah Sharibu Ta Saura Da Rai – Bisa Bayanin Malamin Jami’a Da Aka Sace
Wani Malamin Jami’ar wata kwaleji da wasu mutane goma wadanda kwanan nan ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace su, sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da su daukin matakin ceton su daga hannun ‘yan ta’addan.
Wannan na zuwa ne awanni 24 kacal bayan kisan wasu ma’aikatan agaji hudu da kungiyar Boko Haram ta yi. ‘Yan ta’addan sun sace ma’aikatan agajin ne da a baya aka kashe a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.
3. Kotu ta Ba da hukuncin Karshe akan Gwamna Ganduje Kan Cin Hanci Da Rashawa
Kotun Tarayya da ke zaune a Kano ta yi watsi da wata kara da wani lauya a Kano, Bulama Bukarti ya shigar a gabanta na neman umarnin kotun da ta tilasta wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Kasa Ta’annati (EFCC) don ta binciki gwamna Abdullahi Ganduje bisa zargin karbar cin hancin daga hannun wani dan kwangila.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, arewacin Najeriya, ta yi watsi da karar a ranar Litinin da yamma, 16 ga Disamba saboda “rashin hujja”.
4. Dalilin da yasa DSS baza ta iya sakin Omoyele Sowore ba – Malami
Babban Lauyan Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce ba zai iya ba da umarni ga ma’aikatar ta DSS ba don su saki Omoyele Sowore.
Malami ya fadi hakan ne don mayar da martani ga kiran kalubalai da lauya da kuma mai ba da shawara ga Sowore, Femi Falana (SAN), ya bayar na neman shi da ya umarci ‘yan sanda asirin da su saki Sowore.
5. APC Ta Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Akeredolu, Okorocha da Sauransu
Shugabannin jam’iyyar APC ta kasa baki daya a ranar Litinin sun dage dakatarwar a kan Gwamna Rotimi Akeredolu, Sanata Ibikunle Amosun, Sanata Rochas Okorocha, Mista Osita Okechukwu, da Fasto Usani Uguru Usani.
Jam’iyya mai mulki ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu, wace kuma ta aika wa kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta hannun Sakataren yada labarai na kasa ga Jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu.
6. Sarkin Bichi Na Jihar Kano Ya Tsige Hakimai 5
Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi a jihar Kano, Arewacin Najeriya, ya kori Shugabannin Gundumomi guda biyar a yankin nasa.
Naija News ta samu labarin cewa an cire Shugabannin Gundumomi biyar ne saboda rashin biyayya ga Sarki Aminu Ado Bayero da masarauta bi da bi.
7. Wata Rukuni Na Zargi Fayemi da yin Makirci don maye gurbin Osinbajo da Tsige Oshiomhole
Bangaren yada labarai ta Jam’iyyar PDP a reshen jihar Ekiti, ta zargi gwamna Kayode Fayemi da shirya makarkashiyar maye gurbin Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Litinin ta hannun Bola Agboola, kungiyar ta nemi tsohon Ministan da ya daina shirin tsige Shugaban Jam’iyyar na kasa baki daya, Adams Oshiomhole.
8. Ni Ba ‘Yar Kano Bace, Saboda Haka Ba Ku Da Iko A Kaina – Sadau Ta Gayawa Kannywood
Jaruma Rahama Sadau ta bayyana da cewa shugabancin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa a Kano wace aka fi sani da Kannywood, cewa basu da ikon daukan matakan hukunci a kanta, don ita ba ‘yar Kano ba ce.
Wannan zancen ya fito ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai ya bayar a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba 2019.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Naija News Hausa