Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 20 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 20 ga Watan Disamba, 2019
1. Yan Najeriya Sun Nemi A Tsige Shugaba Buhari
‘Yan Najeriya sun tafi shafin yanar gizo na Twitter don neman tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ya bayar da rahoton cewa, bukatar da ‘yan Najeriya ya biyo ne bayan da Majalisar Wakilai ta Amurka suka dauki matakin tsige Shugaba Donald Trump na Amurka.
2. Interpol Sun Kama Adoke yayin Da Ya Sauka Abuja
Jami’an Interpol sun kame tsohon babban lauyan Najeriya kuma ministan shari’a, Mohammed Bello Adoke a lokacin da ya sauka a Filin jirgin saman kasa da ke a Abuja.
Mike Ozekhome, mai ba da shawara ga Adoke ne ya bada tabbacin hakan.
3. Sowore: Majalissar dattijai ta ba da umarnin kai tsaye Ga Falana, DSS Da Wasu kuma
A ranar Alhamis din da ta gabata ne majalisar dattijan Najeriya ta umarci ma’aikatar DSS, AGF Abubakar Malami da lauyan Omoyele Sowore, Femi Falana (SAN) don gabatar da shaidunsu.
Naija News ta rahoto cewa wadanda aka umarce su da gabatar da shaidu sune Sakataren zartarwa na hukumar kare hakkin dan adam ta kasa (NHRC), Tony Ojukwu Esq, babban alkalin babbar kotun tarayya da kuma alkalin lokacin da aka mamaye kotun, Mai shari’a Ijeoma Ojukwu.
4. Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Bada Hutun Kirsimeti Da Sabuwar Shekarar
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ayyana ranar 25 ga Disamba, 26th da Janairu 1, 2020 a matsayin ranar hutun jama’a don Kirsimeti, Ranar Dambe da kuma Sabuwar Shekara.
An sanrar da hakan ne ta hannun Ministan yada labarai na kasar, Rauf Aregbesola a ranar alhamis, ta hanyar wata sanarwa da sakatare-janar na ma’aikatar cikin gida, Georgina Ehuriah ta fitar.
5. Saraki Ya kare Dimokiradiyyar Najeriya da Hadin Kan kasa – Secondus
Shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party, Uche Secondus, a ranar alhamis, ya bayyana cewa tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya kare dimokradiyyar Najeriya da hadin kan kasa a yayin da yake rike da mukamin shugaban majalisar na 8.
Shugaban PDP yayin da yake taya Saraki murnar ranar haihuwar sa ta shekara 57, ya bayyana cewa tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ceci kasar daga rushewa.
6. Yahaya Bello Ya Rushe Rukunin Majalissar Jihar Kogi Gaba Daya
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a ranar Laraba, ya rushe majalisar ministocinsa.
Gwamna a cikin umarninsa ya ce rushewar na gaugawa ne a yayin da ya umarci duk membobin majalisar da su mikar da duk abin ya shafi ofishin su ga manyan jami’an a ma’aikatunsu daban-daban.
7. Sakon Atiku Ga Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki Na Murnan Shekaru 57 Ga Haifuwa
Tsohon Mataimakin Shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya taya tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki murnar cika shekara 57 da haihuwa.
Atiku wanda ya yi amfani da shafinsa na Twitter domin tayin murna ga tsohon gwamnan jihar Kwara din ya yi addu’ar Allah ya ba shi karin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya.
Ka Samu kari da Cikakken Labaran Najeriya Ta Yau a shafin Naija News Hausa