Connect with us

Labaran Nishadi

Kannywood: Ba na son Auren mai Kudi – inji Jaruma Jamila Nagudu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A fadin Jarumar, “Ba na son Auren mai kudi ko kadan, kuma kazalika ba na son auren talaka”

Jamila Umar Nagudu, shaharariyar ‘yar wasan fim na Kannywood ta bayyana wannan ne a wata zaman ganawa da ta yi da gidan telebijin ‘Kannyflix Programme’ a wajen shirin su na ‘Mujallar Tauraruwa’ 

An haifi Jamila ne a ranar 10 ga Watan Agusta, ko da shike babu tabbacin shekarar da aka haife ta, amma Jamila ta kasance jaruma ce da kuma masoyanta ke murna da ita sosai ga irin kwarewanta a fagen wasan kwaikwayo.

Ganin Jarumar ta isa ta yi aure, kuma kamar yadda ta ke da kyan ganin, za ka iya ransuwa da cewa wata mai girman kai ce ko kuma watakila macce ce mai son kudi sosai.

Amma abin mamaki shine Jamila ta ce “Ba na son auren mai kudi, kuma kazala ba na iya auren talaka, saboda shi mai kudi ba zai ba ni kulawa ta gaske ba ganin irin yada zai yita tafiye-tafiye da fita iri-iri, kuma ba zai iya zuba ma ni soyayya iri da na ke so ba. lokaci zai zama masa kadan wajen kulawa da ni” in ji Jamila.

“Ina son ne in auri mutum wanda zai nuna mani kulawa ta gaske kuma wanda zai biya bukata ta, kuma ya bani lokacin sa” in ji ta.

Jin hakan zaka iya bayyana irin macce da Jamila Nagudu ta ke.

A baya, shekara da ta wuce Jamila a bayanin ta da gidan labaran BBC ta ce “Ibada ne da Shirin fim ne abu mafi muhimanci a waje na” in ji ta.

 

Kara samun labarai akan nishadi a Naija News Hausa

Kalla kuma: Sabon Shiri na Shekarar 2019: “Mubarak” Shafi na daya da shafi nabiyu