Labaran Najeriya
APC: Mutane biyu sun mutu a Jihar Sokoto wajen Rallin Shugaban Kasa
Mun sani rahoto a Naija News Hausa da cewa magoya bayan Jam’iyyar APC biyu sun rasa rayuwarsu a yawon yakin neman zabe da aka gudanar a Jihar Sokoko a ranar Laraba da ta gabata.
Kamar yada muka sanar a baya da cewa mutane da dama sun ji raunuka, wasu kuma sun mutu a Jihar Borno da Yobe sakamakon yawar mutane da suka halarci ziyarar shugaba Muhammadu Buhari wajen yakin neman sake zabe.
Da safiyar nan mun sami labari da cewa Wata mata da wani yaro mai kankanin shekaru goma sha biyar 15, sun rasa rayukansu sakamakon wannan yawon yakin neman zabe da aka yi a Jihar Sokoto.
A halin yanzu ba a gabatar da sunayen wadanda suka mutu ba amma mun sami tabbaci daga jaridar Daily Trust da cewa Matar ta mutu ne sakamakon buguwar mota, a yayin da ake yawo, mota ya hau kanta, Dan yaron kuma an bayyana da cewa ya fadi ne da kansa ya mutu don irin yawar mutane da ke a wurin da dumi.
“Yakin nemar zaben da aka gudanar a Filin kwallon Giginya Memorial Stadium a nan Jihar Sokoto ya tafi ne da rayuwa biyu”.
Za mu sanar da duk wata rahoto da ta biyo baya akan wannan.