Kannywood: Takaitaccen labarin Ummi Ibrahim Zee Zee

Takaitaccen labarin shararriyar ‘yar wasan film na Kannywood da kuma mawaka mai suna Ummi Ibrahim da aka fi sani da wata sunan shiri watau ‘Zee Zee’.

An haifi Ummi ne a Jihar Borno a shekara ta 1989. Tsohon ta Ba’Fullace ne, uwar kuwa ‘yar Arab ce.

Ummi ta bayyana shahararun ‘yan wasa da ta ke ji d su da kuma take koyi da su sosai wajen shiri.

“Wadanda na ke ji da su kuma na ke koyi da su a filin wasan Kannywood sune kamar haka; Marigayi’a Aisha Dan-Kano da Marigayi Rabilu Musa Dan-Ibro. muna ba wa juna girma sosai da gaske, Allah ya gafarta masu” in ji ta a wata ganawa da ta yi da manema labaran (Information Nigeria) shekara da ta gabata.

Tana da kyautannai da dama da ta samu wajen shiri, musanman a wata shiri da ta yi mai suna ‘Jinsi’ a inda ta sami sunan ‘Zee-Zee’, daga cikin wasan ne aka sami mai suna Fati Washa wadda ta jagoranci shirin na ‘Jinsi’. 

Naija News ta ruwaito Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ba zai manta da yan Shirin Fim, Mawaka da Yan Nanaye ba

A halin yanzun, Ummi Ibrahim ba ta saura da shirin fim ba a Kannywood amma shaharariyar ‘yar wasan da kuma mawakar ta samu fita daga shirin fim da dama a Kannywood haka kuma ta na da rakad din wakoki da tayi da dama kamin ta bar Kannywood. Ma soyan ta na yaba mata kwarai da gaske ganin irin hikima da ke gareta a lokacin da take shirin fim.

Kyakkyawar na da kudi sosai kuma har ila yau ba ta da aure. Ta ce “Ina duban nufin Allah ya cika ga me da yin aure na” a ganawan ta da manema labarai shekara da ta gabata.

 

Karanta kuma: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta

Kalla; Ruwan Dare Shafi na Daya da na Biyu