Labaran Najeriya
Ba zan gudanar da neman zabe na ba da tattalin arzikin kasar – inji Buhari
Shugaba Buhari ya ce sam shi ba za ya gudanar da neman zaben sa ba kamar yadda mutanen baya suka saba
Shugaban kasar, Muhammadu Buhari a ranar Laraba da ta gabata ya ce, “ba zani gudanar da shirin neman zabe na ba da tattalin arzikin kasar kaman yadda gwamnatin da ta saba yi” a na su shirin zabe a baya.
Shugaban Muhammadu Buhari ya sake bayyana shirin sa na yaki da kawo karshen cin hanci da rashawa a duk fadin kasar, kamar yadda ake raunana tattalin arzikin kasar wajen gudanar da shirin neman zabe.
Naija News ta ruwaito da cewa Babban Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Jihar Benue, Alhaji Garus Gololo ya bayyana ce wa idan har ‘yan Najeriya suka goyawa Atiku baya har ya hau ga shugabanci, lallai ya tabbata Atiku zai raba kasar biyu.
Garba Shehu, Babban mashawarci na musamman ga shugaban kasa ga yada labarai, ya sanar da wannan ne a karshen taron Majalisar tarayya (FEC) da aka yi a birnin Abuja.
Shugaba Buhari ya umarci ministoci da cewa su yi amfani da na’urar fasaha wajen don kai ga masu jefa kuri’a da ganin cewa sun mayar da shugabancin jam’iyyar APC a zaben 2019 da za a gudanar a watan na gaba.
“Ku yi amfani da samar da sako a waya da kuma hanyar yanar gizo da don neman kuri’a ga jam’iyyar da kuma gwamnatin”.
“Babu kudi da zai fito daga aljihun tattalin arzikin kasar don neman zabe, Ba zan ba da izinin hakan ba, “in ji shi.
Shugaban ya bayyana cewa shirin da Jam’iyyar APC ke da ita ga kasar, shiri ce mafi kyau ga Najeriya don kawo cin gaban tattalin arziki ga kasar.
A baya kuma Naija News Hausa ta samu sanin cewa Sakataran Yada Labarai na Kungiyar APC na da Bolaji Abdullahi ya bada bayani dalilin da ya sa ba Muhammadu Buhari ke cikin Aso Rock ba.
” Ya kamata wannan sakon ya kai ga dukan ‘yan Najeriya cewa ba za mu iya amfani da kuɗi daga aljihun kasar ba don raba wa masu jefa kuri”. ‘Yan Najeriya na bukatar canji kuma mu kaɗai ne za mu iya samar da wannan canji.
Shugaban ya yi amfani da zarafin kuma don yi wa Ministan Harkokin Waje, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim murna da yi mata fatan alkhairi ga takarar zaben da ta fito.
Karanta kuma: Hukumar INEC ta mayar da martani ga jam’iyyar PDP a kan zaɓan Amina Zakari, sun kara da cewa, “PDP ba za su koya masu yadda za su aiwatar da aikin su ba.