Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben 2019: APC na amfani da kayakin Jihohin kasar don kadamar da shirin zaben su – Atiku

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

‘Yan Jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari sun karya doka wajen amfanin da kayakin jijohi don aiwatar da aikin neman zaben 2019

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ‘yan Jam’iyyar sa na zargen ‘yan adawan su, Jam’iyyar APC da dan takarar Jam’iyyar, Shugaba Muhammadu Buhari da yin amfani da asusun gwamnatin jiha don karfafa shirin neman zaben 2019 da ke gaba.

Paul Ibe, daya daga cikin masu samar da labarai ga dan takarar jam’iyyar PDP ya ba da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis a yayin da ya aika ga yanar gizon sa na Twitter @omonlakiki.

Ya kara da cewa Shugaban kasar da Jam’iyyar sa na yin amfani da kayakin jiha ne wajen aiwatar da kamfen din jam’iyyar su da kuma taimakawa Buhari don cin zaben 2019.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Shugaban kasar, Muhammadu Buhari a ranar Laraba da ta gabata ya ce, “ba zani gudanar da shirin neman zabe na ba da tattalin arzikin kasar kaman yadda gwamnatin da ta saba yi

Paul, A cikin fadin sa ya ce “Shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC na karya dokar Hukumar zabe kamar yadda a ka kafa dokar a shekara ta 2010 da cewa kada wani ya yi amfani da kayakin jiha don aiwatar da bukatun sa ko ta yaya” amma Buhari da Jam’iyyar sa sun karya wannan dokar.

Ka tuna cewa a baya kuma “Farfesa Mahmood Yakubu, Babban Shugaban Hukumar Kadamar da Zabe (INEC) a watan Disamba da ta wuce ya bada umurni da ‘yan takara da cewa kada kowa ya yi amfani da kayakin jiha ko wace iri ne don gudanar da aikin neman zabe.

“Tsarufan yada labarai sunna taimaka wa Buhari da Jam’iyyar wajen yi masu kamfen harma da tabbacin rattabawar hannu daga  Hukumar Yada Labarai da Al’adu ta Tarayya har ma suna gabatar da ci gaba da Jam’iyyar APC ta samu a shugabancin ta a jihohi kamar Abia, Kwara, Legas, Ebonyi, Delta da Kano, da sauransu” in ji Paul.

“Wannan mataki ce na Hukumar Yada Labarai da Al’adun ta Tarayya wajen goyawa shugaba Buhari baya don cin nasara ga zabe na gaba.

Muna kira ga Hukumar Kadamar da Zabe (INEC), su dakatar da wannan matakin Hukumar Yada Labarai da Al’adu ta Tarayya da kuma masu Yada Labarai don su janye daga wannan.

 

Karanta kuma:  ‘Yan Jam’iyyar PDP sun ce ba su yarda da Amina Zakari ba a zaman Kwamishanan kulawa da kirgan zabe ta 2019.