Connect with us

Labaran Najeriya

Kungiyar Manyan Jihar Borno, Na Yaba Maku Sosai – inji Atiku

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A gaskiya na yaba maku da rashin amincewa da sake ‘yan ta’addan da aka kame – in ji Atiku Abubakar zuwa ga manyan shugabannan Jihar Borno.

Dan takarar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar na yaba wa Kungiyar Manyan shugabanan Jihar Borno (Elders Forum) don sakon da suka aika wa shugaba Buhari na cewar ya kamata shugaban ya daina halin sake ‘yan ta’adda da aka kame don sun fada da cewa sun tuba, “wanan bai da ce ba” in ji Shugabanan Jihar.

“Shugaba Buhari ya ki amincewa dani a kan na bashi wannan shawarar shekarar 2018 da ta gabata har ma saubiyu” in ji Atiku.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Babban Shugaban kungiyar Miyetti Allah a Jihar Benue, Alhaji Garus Gololo ya ce, “Atiku zai raba kasar biyu idan har ya ci zaben 2019. 

“Wannan bai da wata ma’anar kwarai ga rundunar sojoji har ma ga bayyanar al’umma” inji fadin Atiku.

Ya ce, ya tuna a baya da cewa daya daga cikin shugabannan ‘yan kungiyar Boko Haram, Abba Umar yayi ikirarin cewa idan har aka sake shi, lallai shi zai koma ga kungiyar.

Wannan bayyanin ya fito ne daga bakin mai bada shawara na labarai ga Atiku, Mista Paul Ibe a ranar Asabar da ta gabata a nan birnin Abuja.

A gaskiya har idan aka jefa mani kuri’a har na ci zaben shugaban kasa, ba zani yadda da sake duk wanni dan ta’adda ba da aka kame.

“Maimakon hakan, sai dai ayi masu hukumci wadda ta dace da laifin da suka aika a bisa dokar kasa” in ji Atiku.

Shugabanan sun bayyana rashin amincewar su da matakin shugaba Buhari a fadin cewa “bai dace ba da sake ‘yan ta’adda da aka kame ko da furda da cewa sun tuba ne” in ji Shugabanan zuwa ga shugaba Muhammadu Buhari.

 

Karanta kuma: Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Habiba Usman da zargin sanadiyar sace ta da aka yi