Connect with us

Uncategorized

An Kame Habiba Usman a Jihar Neja da zargin sanadiyar sacewar ta – Yan Sanda

Published

on

at

Habiba Usman da ake zargin ta da sanadiyar yadda aka saceta ta bar gida ne da fadin cewar zata je binciken lafiyar jikinta a ranar 26 ga watan Disamba, shekarar 2018 da ta gabata.

“Ta gaya mani ne da cewa zata je bin ciken lafiyar jikinta” in ji Usman, mijin Habiba.

‘Yan Sanda Jihar Neja sun kame matan auren mai shekaru 20 ne bayan wadanda suka sace Habiba sun karbi kudi kimanin dubu dari da hamsin N150,000 a hannun mijinta don su sake ta.

“Sun bukace ni ne da biyar Miliyan hudu (N4m)” in ji Usman Alfa.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘Yan Sandan kasar China sun kame wani matashin Najeriya mai suna Uzoma Joseph da sana’ar sayar da mugayen kwayoyi a kasar China.

Ya ce, sun ce in biya miliyan hudu ne da farko, amma na kasa. Bayan gwagwarmaya na da rokon da na yi, shi ne suka karbi dubu dari da hamsin N150,000 daga gareni.

‘Yan sanda da ke yankin Bosso yankin Minna ta Jihar Neja da Jami’an tsaro da ke bincike da yaki da halin sace-sace ta Jihar ne suka kama Habiba Usman tare da mutum biyu da ake zargin su da aikata mugun halin; sunayan su na kamar haka:

  • Abubakar Umar da shekaru 28 dan anguwar Chanchaga
  • Musa Abubakar kuma na da shekaru 22 daga Sauka Kahuta, Minna, Jihar Neja.

‘Yan Sanda sun ce Malam Usman Alfa da ke a garin Beji ta yankin karamar hukumar Bosso a Jihar Neja ya kawo kara ne a ranar 28 ga Watam Disamba, 2018 cewa matarsa, Habiba ta bar gida ne tun ranar 26 ga Watan Disamba, 2018 da cewar za ta je asibiti don binciken lafiyar jikinta a Asibitin Tarayya da ke garin Minna amma ba ta dawo gida ba tun lokacin.

Usman ya bayyana wa ‘Yan Sanda cewa ya samu kira ne daga ‘yan ta’addan da bukatan ya biya kudi naira miliyan hudu idan yana son ya gan matar.

“Na kuwa biya su naira dubu dari da hamsin bayan roko da kuka don su sake ta” in ji Usman.

An ci gaba da bincike a kan wannan ……..

Karanta kuma: Wasu ‘yan hari sun kai farmaki a wani kauyen da ke a yankin Kuje  inda suka harbe mutum uku bayan basu cin ma wanda suka je nema ba.