Connect with us

Labaran Najeriya

PDP: A karshe dai Atiku ya shiga kasar Amurka

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan tsawon shekaru goma shabiyu da aka hana wa dan takarar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar shiga kasar Amurka, sai ga shi a jiya Alhamis 17, Janairu, 2019 dan takaran ya aika a yanar gizon nishadin sa da hoton shi da babban shugaban sanatocin kasar Najeriya, Bukola Saraki a kasar Amurka bayan rabuwar su da kasar Najeriya da maraicen ranar Laraba 16 ga watan Janairu.

Kalli hoton a kasa;

Dan takaran da aka ce bai da damar shiga kasar Amurka da baya ya karya wannan fadin.

Mun sami rahoto da safen nan kuma da ganawar da Atiku ya je yi a kasan Amurka da manyan shugabannai akan neman zabe.

Naija News ta ruwaito da cewa, Atiku yayi barazanar da rantsuwa cewa zai sayar da kamfanin man fetur (NNPC), idan har ya hau mulki.

Ya ce “Na rantse ko da za a kashe ni ne sai na sayar da NNPC, an mayar da kamfanin kamar kamfanin ‘yan Mafia” inji Atiku.

Karanta kuma: Ban yi zaton zan fadi ga zaben 2019 ba – inji Shugaba Buhari