Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Bindiga sun kashe Yayar Kabiru Marafa, Sanatan da ke wakiltar Zamfara ta tsaka

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sabuwa:

‘Yan hari da bindiga sun aiwatar da wata sabuwar hari a Jiahr Zamfara.

Wasu mahara kimanin mutum dari sun fada wa kauyan Ruwan Bore da hari har sun kashe ‘yar uwar Kabir Marafa, Sanatan da ke wakilcin yankin Zamfara ta Tsaka, sun kuma sace Mijinta.

A bayanin wani mai suna Abubakar Tsafe ga manema labarai, Ya ce “Maharan sun fada wa gidan Sanatan ne inda ‘yar uwansa ke zama a Ruwan Bore ta karamar hukumar Gusau a yau Talata” Abubakar ma’aikaci ne a gidan Sanata Marafa.

“Kusan rabin girman kauyan Ruwan Bore ta kama da wuta a sakamakon wannan harin. Jama’ar kauyan duk sun shiga kauyan Mada don gudun Hijira” inji Abubakar Tsafe.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Mahara da Bindiga sun kai sabuwar hari a wata Gidan Kallon wasa a Jihar Zamfara

Kimanin mutane bakwai ne aka sace a lokacin da ‘yan hari da bindigan suka fada wa gidan kallon wasar makonnai biyu da ta gabata a nan yankin Birnin Magaji ta Jihar Zamfara.

“Sun kai kimanin mutane 20 da suka hari gidan kallon, Isowar su a wajen kallon misalin karfe 10:00 na dare, sai suka tambayi mai jagoran Gidan kallon, ni kuma da jama’ar da ke wajen muka amsa masu da tunanin cewa jami’an tsaro ne ba tare da sanin cewa ‘yan hari da bindiga ne ba” in ji Mallam Sanusi.

Mun sanar a Naija News Hausa da cewa, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawalin magance hare-haren ‘yan ta’addan a Jihar Zamfara idan har an zabe shi kuma ya lashe tseren shugaban kasa ga zaben 2019.