Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Karanta Jawabin Shugaba Muhammadu Buhari bayan da ya lashe zabe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar APC ga tseren zaben shugaban kasa ta shekarar 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya yi gabatarwa bayan da hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta gabatar da shi a matsayin mai nasara ga tseren zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.

Mun gane a Naija News da cewa an shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben kujerar shugaban kasa bayan da sakamakon kuri’u ta nuna da cewa Buhari ya fiye dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar da kuri’u.

Ga gabatarwan shugaba Muhammadu Buhari kamar haka;

1. A farko dai ina mai godiya ga Allah da ya bamu rai da kuma bada nasara ga siyasar kasar Najeriya a wannan shekara, musanman yadda muka samu nasara a Jam’iyyar mu ta APC.

2. Ina kuma nuna godiya na ga Al’ummar Najeriya da suka fita don sake jefa kuri’ar su gareni don ganin cewa na ci nasara ga tseren takaran shugaban kasa na bana, da kuma bani daman shugabanci a shekaru hudu ta gaba.

3. Ina kuma kai gaisuwa na ga jigo da shugaba na Jam’iyyar APC ta tarayya, Asiwaju Bola Tinubu da irin gwagwarmaya da goyon baya da ya bani a matsayin shugaban Jam’iyya. Na koma gode wa jagoran lamarin siyasa na Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da mai gudanar da hidimar yakin zaben jam’iyyar, Rotimi Amaechi, hade da dukan mambobi na Jam’iyyar APC gaba daya.

4. Godiya ta musanman ga wadanda suka bayar da jarin su ga hidimar yakin neman sake zaben, musanman a kasa irin Najeriya. Nagode kwarai da gaske.

5. Ina mai nuna godiya kuma ga yawar mutane da suka bayar da lokacin su da kuma kan su domin wannan hidimar zaben ta kai ga nasara, ba ni da isashen kalamai da zan iya gode maku. Allah ya biya ku duka.

6. Ko da shike a gudanar da zaben a cikin kwanciyar hanjali da kuma hanya da ta dace, mun gane da cewa wasu ‘yan tashin hankali sun tayar da tanzoma da farmaki a wasu yankuna. Jami’an tsaro zasu tabbatar da cewa sun dauki matakai da ya dace akan wadannan.

7. Ina mai bakin ciki da kuma raunana da wadanda suka rasa rayukan su a yayin da ake gudanar da hidimar zaben. hukumomin tsaro zasu dauki mataki ta musanman ga zabanni ta gaba.

8. Ina kuma godewa hukumomin tsaro da irin yadda suka tafiyar da ayukan tsaro a lokacin zaben. Na jinjina masu da samar da tsaro musanman a cikin lokaci mai tsanani kamar haka.

9. Ina kuma bada shawara da bukatar mabiya bayana da cewa kada su tsananta, ko nuna halin cin mutunci ga ‘yan adawarmu. Cin nasaran zaben kawai ya isa abin riba gareku duka.

10. Godiya ta musanman kuma ga masu hangen nesa daga kasar waje da kuma nan kasar mu da irin gwagwarmaya da kuma kokari da suka yi duka wajen hidimar zaben kasar mu.

11. Gwamnatin mu za ta karfafa tsaro da kuma sake tsarafa tattalin arzikin kasar da kara yaki da cin hanci da rashawa musanman kamar yada muka fara a baya da ganin cewa mun kai ga cin nasara da hakan.
Zamu kuma tabbatar da cewa mun karfafa zamantakewar mu a kasar don ganin cewa babu wanda aka manta da shi a kowace shiyya.

12. Na gode maku da goyon baya, Allah ya albarkaci kasar Najeriya.

Karanta wannan kuma: Kalli bidiyon Demola, da aka yiwa jifa da duwatsu a Jihar Legas ya saura da rai