Uncategorized
Aminu Shagali ya lashe kujerar Gidan Majalisar Jihar Kaduna daga Jam’iyyar APC
Kakakin yada yawun Gidan Majalisar dokoki ta Jihar Kaduna, Aminu Abdullahi-Shagali, ya sake lashe kujerar gidan majalisar a karo ta biyu ga zaben Gidan majalisa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Malamin zaben jihar ga zaben ranar Asabar, Kamilu Sarki-Labaran daga makarantar jami’a ta Ahmadu Bello University Zaria, ya gabatar a rahoton sa da cewa Shagali ya lashe tseren takaran ne da kuri’u 36,431.
Ya bayyana da cewa dan takaran ya lashe kujerar gidan majalisar ne da kuri’u fiye da sauran ‘yan takara daga jam’iyu tara. babban dan adawan sa daga jam’iyyar PDP, Kasimu Lawal-Abdullahi, na da kuri’u 15,268. Na kusa gareshi daga jam’iyyar PRP, Fahad Ahmad-Chikaji na da kuri’u 270.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Alhaji Umaru Sambawa ya lashe kujerar Gidan Majalisar Jihar Kebbi da kuri’u 40,180.
Karanta wannan kuma: Yan Sandan Jihar Kano sun ci karo da Motar Sienna cike da takardun zabe