Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: ‘Yan Hari da bindiga a yau sun kashe dan shekara 6, da kuma sace mutane ukku a Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Talata, da safiyar nan, ‘yan hari da bindiga a Jihar Katsina sun kashe dan shekara 6 da kuma sace mutum ukku a wata sabuwar hari a garin Kankara.

Rahoto ta bayar da cewa mumunar harin ya faru ne da safiyar yau, a yayin da ‘yan hari da bindigan suka hari daidai gidan Malam Adamu da ke a Kofar Yamma, a nan anguwar Matsiga, inda ‘yan harin suka kashe yaron mai shekara 6, suka sace mutum ukku da kuma barin wani yaro mai shekaru 8 da raunin bindiga.

Naija News Hausa ta gane kamar yadda aka bayar a wata sanarwa da cewa yara biyun na daga zuriyar Malam Adamu ne. An kuma bayar da cewa an sace Malam Adamu ne tare da wasu ‘yan mata masu shekaru tsakanin 18 zuwa 20.

Ko da shike ba cikakken bayanin tukunna game da harin, amma an bayyana da cewa abin ya faru ne missalin karfe daya da rabi (1:30am) na safiyar yau, inda ‘yan harin suka fada wa anguwar da kuma sace kayakin masu tsadar gaske bayan da suka sace mutane ukkun da kuma kashe dan ‘yaron mai shekara 6.

An bayyana da cewa a yayin da ‘yan harin suka hari gidan Mallam Adamu, sun yi kokarin dauke yaran, amma matar Malam Adamu ta yi kokarin hana su. “Da ran su ya baci na ganin cewa matan Malam Adamu na kokarin hana su wuce wa da yaran, sai suka harbe daya daga cikin su anan take, suka kuma yiwa yaro na biyun rauni da bindiga” inji bayanin wani mazaunin wajen a bayanin sa da manema labarai.

Ba a samu tabbaci da kuma bayani ba daga jami’an ‘yan sandan yankin a lokacin da aka karbi wannan rahoton.