Connect with us

Labaran Najeriya

Ba ruwan Buhari da sakamakon zaben ranar Asabar ta gaba – inji Shugabancin kasa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Lahadi, 17 ga watan Maris da ta gabata, shugabancin kasa ta mayar da martani game da zancen cewa watakila shugaba Muhammadu Buhari zai taimakawa gwamnonin Jam’iyyar APC don ganin cewa sun lashe zaben su.

Shugabanci ta gayawa ‘yan jam’iyyar APC duka da cewa “Ku yi watsi da duk wata zance ko tunanin cewa shugaba Muhammadu Buhari zai sa baki ko taimaka da ganin cewa anyi makirci. Hakan ba zai faru ba, shugaba Buhari ba irin wannan mutumi ba ne”

Shugabancin ta kuma gargadi shugabannan jam’iyoyi da janye wa duk wata furcin da zai jawo tashin hankali ko farmaki a gaban zaben ranar Asabar ta gaba a sauran jihohin kasar.

“Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa, INEC ce ke da fadi ta karshe da izini akan zaben kasar, ba shugaba Buhari ba, kuma shugaban ba zai kafa bakin shi ba ga wannan zancen ko taimakawa  wajen kadamar da makirci don jam’iyyar APC ta lashe zaben” inji shugabanci.

Hukumar INEC a baya ta ce “Ba zamu zubar da amincin mu ba don wata tsanani ko damuwa daga wata jam’iyya”, kamar yadda Naija News Hausa ta bayar a baya.

Shugabancin kasar ta gabatar ne da wannan da jin jita-jita daga wasu shugabannai jam’iyoyi na cewar shugaba Buhari zai yi amfani da Ofishin sa don taune hakin ‘yan takara, ko kuma taimaka wa gwamnonin jam’iyyar APC da makirci don ganin cewa sun lashe kujerar takaran.

“Wasu na tunanin cewa shugaba Buhari zai yi amfanin da karfin Ofishin sa don taune hakin ‘yan takara da sauran jam’iyya don ganin cewa hukumar INEC ta juya sakamakon nasarar zaben ga jam’iyyar APC. wannan ba zai kasance ba, Buhari ba irin wannan mutumin ba ne” inji fadin shugabanci kasa.

Shugabancin ta fadi hakan ne a wata gabatarwa da, Mista Garba Shehu, Kakakin yada yawun shugaban kasa ya rattaba hannu.

“An san shugabannan kasar da suka yi shugabanci a baya da irin wannan hali na kafa baki ga irin wannan zabe, amma shi shugaba Buhari ba irin wannan shugaba ba ne. Ya rantse da kare dokar kasa da mutanen ta, ba zai kuma karya wannan ba” inji rahoton.

 

Karanta wannan kuma: Aikin mu na kare yancin Al’umma ne, ba kisan kai ba – inji Yan Sandan Jihar Kano