Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben 2019: Atiku na barnan lokacin shi ne kawai – Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A wata sanarwa da Mista Niyi Akinsiju, Ciyaman na Kungiyar yada labarai ga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Sakataren kungiyar, Cassidy Madueke suka rattaba hannu a ranar Litini da ta gabata a Abuja, babban birnin tarayyar kasa; Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa dan takaran kujerar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, “Atiku Abubakar na barnan lokacin shi ne da kuma lokacin kotun kara kawai.” inji shi.

“Atiku ba zai iya cin nasara ga karar da yake yi ba kan zaben 2019. Dalili kuwa itace, bai da wata shaidar kwarai ko muhinmin bayani da zai bayar ga kotun kara don cin nasara ga zargin da yake yi”

“Barnan lokaci ne kawai yake yi, bai da wata bayanin da zai mika ta musanman”

Kungiyar Yada labarai ga shugaba Muhammadu Buhari (MBO) sun kara da cewa, dan takaran, Atiku, ya sani tun da farko da cewa ba zai iya cin nasara ga shugaba Buhari ba ga zaben shugabancin kasar Najeriya.

“Kokarin kawai yake ya bata wa ‘yan Najeriya lokaci, shi ma ya san ba zai iya lashe zaben ba” inji su.

“Ko da ace za a gudanar da zaben shugaban kasan Najeriyar ne sau goma tsakanin Atiku Abubakar da shugaba Muhammadu Buhari, Atiku ba zai taba cin nasara ba ko sau daya cikin goma”

Sun kara da cewa sakamakon zaben shekarar 2019 ya bayyana ne kawai da cewa mutanen kasar ba su kaunan mataimakin tsohon shugaban kasan.

“Faduwar Atiku ga zaben 2019 ya fara ne daga gidansa’’ inji Mista shugaba Buhari.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Atiku Abubakar ya gabatar da cewa hukumar INEC sun rage masa yawar kuri’u ga zaben 2019 daga cikin kwamfutan su.