Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben 2019: Jam’iyyar PDP ta lashe zaben kujerar Gwamnan Jihar Bauchi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A karshe, bayan gwagwarmaya da jaye-jaye akan zaben kujerar gwamnan Jihar Bauchi; Hukumar gudanar da zaben kasar Najeriya (INEC), a yau Talata, 26 ga watan Maris 2019 ta gabatar da Sanata Bala Mohammed, dan takaran gwamnan Jihar daga Jam’iyyar PDP a matsayin mai nasara ga zaben 2019.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kotun Koli ta umurci Hukumar INEC da cewa kada hukumar ta gabatar da sakamakon zaben gwamnan Jihar Bauchi.

Babban Malamin zaben da ke jagorancin zaben yankin karamar hukumar Tafawa Balewa, Dakta Musa Dahiru daga Makarantan Jami’a Fasaha babba ta Kashere, ya gabatar da cewa dan takaran jukerar gwamnan Jihar Bauchi da jam’iyyar PDP, Bala Mohammed ya samu yawar kuri’u 39,225. Shi kuma Gwamnan Jihar, Mohammed Abubakar na da kuri’u 30, 055 a karamar hukumar Tafawa Balewa.

Wannan sakamakon ya bayyana da cewa Bala Mohammed ya lashe zaben Jihar da yawar kuri’u 515,113 a dukan kananan hukumomin Jihar, bisa dan adawan sa da ke da yawar kuri’u 500,625.

Karanta wannan kuma: Dalilin da ya sa Shugaba Buhari yayi watsi da neman zabe ga Gwamnonin APC