Connect with us

Labaran Najeriya

Karya ce kuri’un da Buhari ya samu ga zaben 2019 – inji Buba Galadima

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Buba Galadima, Kakakin yada yawu ga lamarin yakin neman zaben Alhaji Atiku Abubaka, dan takaran shugaban kasa ga zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, ya kara bayyana da cewa kuri’un da hukumar INEC ta gabatar na shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019 ba gaskiya bac ce inji shi.

Galadima ya fadi hakan ne don goyon bayan zargi da barazanar da Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) ke yi na cewar sun fiye Jam’iyyar APC da kuri’u ga zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar nan ga zaben 2019.

“Hukumar INEC ta gabatar da sakamakon da ta gamshe su ne kawai, Muna kuma da daman bayyana rashin amincewar mu da wannan sakamakon da hukumar ta gabatar da shi. Zamu kuma bayar da tamu shaidu idan mun kai ga kotun kara, ba ga ‘yan kasar Najeriya kawai ba, amma har ga duniya gaba daya; zamu tabbatar da cewa kowa ya gane irin makirci da halin taunewa da aka nuna wajen zaben kasar Najeriya ta shekarar 2019.

“Da irin tabbaci da shaidu da muka riga muka tara akan hidimar zaben, duk ta bayyana da cewa dan takaran mu, Alhaji Atiku Abubakar ne ya lashe tseren zaben shugaban kasa ta shekarar 2019, Wannan zai kuma bayyana ga ‘yan Najeriya duka a gaban kotu”

Buba ya gabatar ne da hakan a wata tattaunawa da yayi da gidan talabijin na Channels TV

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Buba Galadima ya zargi APC da kashe naira Miliyan 45 ga yankuna don ‘sayen hankalin mutane ga fitar ralin Buhari