Connect with us

Labarai Hausa

Abdulrahman yayi Barazanar Kashe Kadaria Ahmed don janyewa daga Musulunci

Published

on

Wani mai suna Abdulrahaman Yahaya ya zargi Kadaria Ahmed, shahararrar ‘yar watsa labarai da janyewa daga Addinin Musulunci zuwa Addinin Kirista.

A bayanin sa, ya ce “Abin takaici ne da na ji da cewa Kadaria ta koma ga addinin Kirista. Duk da cewa ta kira kanta ‘yar Jihar Zamfara.”

“Ba ta da zarafi da damar kiran kanta ‘yar Zamfara da wannan mataki da ta dauka na janyewa daga Addinin Musulunci zuwa ga Addinin Kiristanci.”

Abdulrahman,  a garin nuna bacin ransa da fusata, ya aika da wannan a shafin yanar gizon nishadarwa ta Twitter na sa inda ya ce da ita “fankon gawa da ke da suffar mai rai”

“Ya kamata ne a kashe ki a matsayin yin ridda, saboda janyewa daga Addinin Musulunci” inji shi.

Naija News Hausa ta gane da cewa Abdulrahman ya fadi hakan ne bayan da ya gane da zargi da zagin da Kadaria ta yi ga Gwamnan Jihar Zamfara a kwanakin baya.

Kalli sakon a kasa kamar yadda Abdulrahaman Yahaya ya aika a layin Twitter;

Ko da shike, kanwar Kadaria, watau Matar Gwamnan Jihar Kaduna ta gabatar da cewa ba gaskiya ba ne, “Kadaria ba ta janye daga Addinin Musulunci ba, Kuma bata koma ga Addinin Kiristanci ba” inji ta.