Connect with us

Uncategorized

Ga sabuwa a Kannywood: Ali Nuhu yayi karar Adam A. Zango a Kotu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shahararrun Manya daga cikin ‘yan fim na Kannywood biyu sun shiga kafar wando guda

Naija News Hausa ta gano da wata bidiyon da ya bayyana da cewa Ali Nuhu da Adam A. Zango na fada da junar su.

Mun sanar a baya da cewa Hadiza Gabon tayi fada da Amina Awal a fagen shirin fim. An bayyana da cewa tayi fada da jayayya da Kyakyawa da kuma Shahararar ‘yar shirin fim, Nafisa Abdullahi a kwanakin baya a fagen shirin fim.

Ali da Adam abokai ne a da a fagen shiri. amma mun gane kwanakin baya da cewa wata abu ta shiga tsakanin su, har ga rabuwa da magana da juna.

Ko da shike an bayyana da cewa Adam ya gabatar da cewa fadan ya kare, amma abin mamaki sai gashi an gano wata takardan Kotu da Ali Nuhu ya wallafa na zargin cewa Adam A. Zango na bada masa suna.

Kalli bidiyon a kasa;

Karanta wannan kuma: Karanta Takaitaccen Labarin rayuwar Sani Danja