Labaran Najeriya
Majalisar Wakilai sun bukaci Buhari da bayyana a gidan majalisa cikin awowi 48
Gidan Majalisar Wakilan Jiha sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari da bayyanar da kansa a zaman Majalisar don gabatar da sanadiyar kashe-kashen da ake yi a Jihohin kasar.
Majalisar ta bada daman awowi 48 ne kawai ga shugaban da yin gabatarwa ga al’ummar kasan game da sanadiyya da kuma mafarin kashe-kashen da ke aukuwa kasar.
Gidan Majalisar ta dauki wannan mataki ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu da ya gabata, da zargin cewa shugaban ya kasa ga shugabancin sa, musanman kare rayukar al’ummar kasar da abin zaman su.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hadaddiyar Kungiyar Kiristocin kasar Najeriya, CAN sun shawarci shugaba Muhammadu Buhari da karfafa hukumomin tsaron kasar Najeriya.
Gidan Labaran nan ta mu ta gane da cewa Jihohin kasar Najeriya musanman Jihar Zamfara, Kaduna, Nasarawa da Borno na fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda kusan kowace sa’a da barnan kayakin mutane da kashe rayuka.
A ganin hakan ne Gidan Majalisar Wakilan suka gabatar da bakin cikin su da yadda jihohin suka koma. Musanman rayukar da suka mutu sakamakon hare-hare.
Majlisar sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari da bayyanar da kansa a gaban gidan Majalisar don gabatar ga Al’ummar kasar Najeriya irin mataki da shirin da ya ke kan dauka don magance yanayin hare-hare da ake ciki a kasar.
Majalisar sun kara da bukatar shugaban da basu tabbacin zargin da ake na cewar Manyan Sarakunan kasa, ‘yan ruwa da tsaki da kuma masu haƙa ma’addinai ne ke karfafa ta’addanci a kasar.