Connect with us

Labaran Nishadi

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta bayar da Jami’an tsaro 1,350 don tsaro ga Sallar Easter

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Neja ta gabatar da cewa zasu watsar da Jami’an tsaron hukumar su guda 1,350 a yankunan da ke a Jihar Neja don tabbatar da tsaro da zaman lafiya, musanman a yayin da Sallar Easter ya gabatao.
Naija News Hausa ta sanar a yau a Manyan Labaran kasar Najeriya da cewa Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ranar Jumma’a 19 zuwa ranar Litini, 22 ga watan Afrilu a matsayin ranar hutu ga Ma’aikata duka don hidimar Easter da za a yi.

Naija News Hausa ta gane da sanarwan samar da ‘yan sanda 1,350 ne don tsarin Jihar, kamar yadda Mista Sabo Ibrahim, Kwamishanan Hukumar ‘yan Sandan Jihar Neja ya bayar ga manema labarai a wata ganawa da suka yi a babban birnin Jihar, Minna, a ranar Laraba da ta gabata.

“Zamu samar da Jami’an tsaro a Ikklisiyun da ke Jihohin da kuma wajajen nishadi da hutu da ke a yankunan don magance duk wata matsalar da ke iya taso wa,” inji Sabo.

Ranar 19 zuwa ranar 22 ga watan Afrilu ya kasance rana ne ga Kiristocin kasar duka don kadamar da Sallar Easter, (Watau tunawa da ranar Mutuwa da tashin Yesu; Isah Almasihu) a dukan kasashe duniya.

“An riga an bada umarnin kadamar da tsaron a Kananan hukumomi 25 da ke a Jihar.”

Kwamishanan Hukumar ya gargadi al’umamr Jihar duka da yin hankali da kuma kasance a hake don sanar ga Jami’amn tsaro da duk wata alamun tashin hankali ko Farmaki a yayin da ake cikin hidimar Easter.

Karanta wannan kuma: Kalli Yadda aka yi wa wani Soja da ke kokarin ‘kare wani daga bakin Mutuwa