Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya sun ci nasara da kashe ‘yan ta’adda Ukku a Jihar Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rukunin Sojojin Saman Najeriya sun yi sabuwar ganawar wuta da ‘yan ta’adda a Jihar Zamfara

Naija News Hausa ta samu rahoto ne da cewa sojojin sun ci nasara da kashe ‘yan ta’adda ukku a wata ganawar wuta da su ka yi da ‘yan ta’addan da suka hari kauyukan Rafi da Doka, a karamar hukumar Gusau ta Zamfara.

Bisa bincike da ganewar Manema labarai, sojojin sun samu kashe Ukku ne daga cikin ‘yan ta’addan.

Rundunar Sojojin sun bayyana da cewa sun gana da ‘yan ta’addan bayan wata hari da suka kai a kauyuka biyu da ke a yankin Mada ta karamar hukumar Gusau.

Kamfanin Yada labaran nan ta mu ta gane da cewa Jihar Zamfara na daya daga cikin Jihohin kasar Najeriya da ke fuskantar hare-hare da sace-sacen mutane. Duk da kokarin hukumomin tsaro a kasar sai karuwa ake da rasa rayuka a kullum.

Ba a Gusau kawai ba, an bayyana da cewa ‘yan ta’addan sun fada cikin kauyukan Rukudawa, Jaja da Tsanu, harma sun hade da mazaunan wajajen da jawo ruduwa.

Ofisan Yada yawu ga Rundunar Sojojin Jihar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya bada tabbacin cewa jami’an tsaro sun yi nasara da kashe Ukku daga cikin ‘yan ta’addan a ranar Laraba da ta gabata a Gusau.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Sarakan Jihar Zamfara na zargin Rundunar Sojojin Sama da kashe mutane a banza.

Kungiyar Sarakan sun gabatar da zargin ne a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu da ta gabata a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru ya gabatar a bayanin sa da cewa Rundunar Sojojin sun aika bama-bamai a wasu shiyar da ba ‘yan ta’adda ke ciki ba.